Yaƙin neman zaɓen Chadi da 'yan damben Tunisiya cikin hotunan Afirka

.

Asalin hoton, YASSINE GAIDI/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Tsoffin ƴan damben El Djem na Tunisiya sun bude fagen farfaɗo da al'adun gargajiya
An wallafa
.

Asalin hoton, JORIS BOLOMEY/AFP

Bayanan hoto, Ranar Juma'a a Chadi, mata sun chaɓa ado da mayafai launin tutar ƙasar yayin da suke dakon shugaban riƙon ƙwarya Mahamat Idriss Déby Itno a wurin yaƙin neman zaɓe.
.

Asalin hoton, KHALED DESOUKI/AFP

Bayanan hoto, Jagoran Addinin Kirista na watsa wa dandazon mabiya daga ƙasashen Masar da Habasha ruwa mai tsarki lokacin ibada cikin wani fitaccen kogo.
.

Asalin hoton, KHALED DESOUKI/AFP

Bayanan hoto, Mabiya Addinin Kirista cikin farin ciki bayan an watso musu ruwa mai tsarki.
.

Asalin hoton, TIKSA NEGERI/REUTERS

Bayanan hoto, Kashegari aka gudanar da shagulgulan ranar Palm Sunday ta mabiya addinin na Kirista.
.

Asalin hoton, FRANCOIS NEL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Laraba ƴan wasan Kuruket a ƙasar Uganda Ritah Musamali da Stephanie Nampiina sun taya juna murna bayan samun nasara a gasar kofin duniya ta mata.
.

Asalin hoton, OSCAR DEL POZO/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, An karrama ɗan wasan ƙwallo Kylian Mbappé ta hanyar zana hotonsa a Madrid babban birnin ƙasar Spaniya.
.

Asalin hoton, FADEL SENNA/AFP

Bayanan hoto, Wani mutum na duba rigunan ƴan wasan ƙwallon ƙungiyar RS Berkhane a ranar Juma'a. Bayan an karɓe rigunan daga wasu ƴan wasan Morocco sakamakon hoton alamar yankin Yammacin Sahara da ake rikici a kansa.
.

Asalin hoton, NACER TALEL/GETTY IMAGE

Bayanan hoto, A ranar ne kuma Kevin Murphy na ƙungiyar Al Ahly Ly ya fafata da ƙungiyar ƴan wasan raga ta City Oilers a wasannin ƙasashen Afrika.
.

Asalin hoton, FADEL SENNA/AFP

Bayanan hoto, A ranar Talata kuma ƙwararriyar mawaƙiya ƴar ƙasar Amurka Jazzmeia Horn ta rera waƙa yayin bikin ranar mawaƙa ta duniya a Morocco.
.

Asalin hoton, DANIEL IRUNGU/EP

Bayanan hoto, Waɗanda suka tsallake rijiya da baya a Kenya na kallon irin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi.
.

Asalin hoton, MAHMOUD ELKHWAS/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Kafin faruwar ambaliyar ruwan, tsuntsaye sun yi shawagi kan masu kamun kifi a gabar tekun bahar rum