Wasu dattawan Arewa sun ce sun koma bayan Atiku Abubakar

Atiku Abubakar
Bayanan hoto, Atiku Abubakar
An wallafa

Wasu da suke yi wa kansu lakabi da kungiyar shugabannin al'ummar arewacin Najeriya sun ce sun  yanke shawarar zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

`Yan kungiyar, wadda suka ce ta kunshi Musulmi da Kirista sun dauki wannan matakin ne don nuna rashin amincewarsu da abin da jam`iyyar APC ta yi na tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimaki.

 

Jiga-jigan kungiyar shugabannin al`ummomin arewacin Najeriyar, sun ce tafiyar tasu ta Musulmi da Kirista ce daga jam`iyyun siyasa daban-daban.

Kuma sun bayyana cewa sai da suka dauki lokaci suna tuntuba tare da nazarin siyasar kasar, musamman ma manyan jam`iyyu da masu yi musu  takarar shugaban kasa, kana suka yanke shawarar mara wa na jam`iyyar PDP baya.

A cewarsu babu adalci a tsarin da jam`iyyar APC ta yi na hada Musulmi da Musulmi a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimaki.

 

Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Sokoto Alhaji Muktari Shagari wanda yana cikin jagororin kungiyar ya shaida wa BBC cewa kungiyoyin sun yi la'akari da hakki na kowa da kowa  da yadda tsarin zama na kasar yake.

 

Ya ce, ‘’Idan kungiyoyin siyasa za su tsayar da ‘yan takara, suna la'akari da hakki na kowa a Najeriya da yadda tsarin zamanmu yake  …Musulmi da Kiristoci.''

''Ba za mu yarda a yaudare mu ba saboda haka da Kiristocin Najeriya da Musulmin Najeriya mu hada kai mu zabi  wannan jam'iyya da wannan dan takara Alhaji Atiku Abubakar da mataimakinsa.” In ji shi.

 

‘’Su ne  suka nuna cewa lallai-lallai babu shakka za a yi wa kowa adalci a cikin wannan kasa tamu ta Najeriya,’’ a cewarsa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kungiyar ta yi  misali da  wasu jihohi da ke da gwamna Musulmi da mataimaki Kirista wadanda suka hada da Adamawa da Osun . 

 

Dattawan arewan sun yi amannar cewa kauracewa jam’iyyar da suka yi saboda hadin da ta yi na takarar shugaban kasa zai yi tasiri kan jam’iyyar ta APC ta yadda ba za ta yi nasara ba.

 

Farfesa Doknan Sheni, wanda tsohon shugaban jami`ar Jihar Filato ne  ya ce sun hada kai ne domin  ta wannan hanyar ce kawai za su iya samun nasara.

 

 ''Da mun hada kai dole za mu ci zabe, APC ba za ta ci zabe ba,  APC za ta ci zabe ne kawai idan ba mu hada kai ba, ” in ji shi.

 

Ya kuma yi ikirarin cewa  suna da magana ne da yawun dukkan Kirista da ke  Arewa.

 

Sai dai wanann abu ne mai wuya a tabbatar saboda akwai wasu Kiristoci da  har yanzu  suna tare da dan takarar jam’iyyar APC.

 

 

Cikin manyan wannan kungiya da suka rada mata suna kungiyar shugabannin al`ummomin arewacin Najeriya har da tsohon kakakin majalisar wakilai, Hon Yakubu Dogara.