Amurka da Burtaniya ba su yarjewa Ukraine amfani da makaman da take so ba a kan Rasha

Tattaunawa tsakanin Amurka da Burtaniya

Asalin hoton, PA Media

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Shugaba Biden da kuma firaiministan Burtaniya sun yi kyakkyawar tattauna a kan Ukraine, to amma ba su sanar da wani mataki a game da bukatar Ukraine na amfani da makami mai cin dogon zango a kan Rasha ba.

Keir Starmer, ya ce ganawar da suka yi a fadar gwamnatin Amurka ta kunshi abubuwa da dama ba abu guda kawai suka mayar da hankali ba.

Da yake tattaunawa da manem labarai, ya musanta cewa shugaba Vladimir Putin, ya yi wa shugabannin kungiyar tsaro ta NATO barazanar cewa zai dauki mummunan mataki idan har aka janye dokar takaita amfani da makami mai cin dogon zango.

Tun da farko jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vassiy Nebenzia, ya shaida wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa muddin aka ba wa Ukraine dama, to kasashen kungiyar su tabbatar sun takalo kazamin yaki.

Ita ma fadar gwamnatin Amurkan ta ce dukkanninsu shugabannin sun nuna matukar damuwa a kan yadda Iran da Koriya ta Arewa ke ba wa Rasha makamai.

A nasa bangaren, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya kara nanata kira ga kasashen yamma kawayensa da su bashi damar amfani da wadannan makamai, yana mai cewa yin hakan shi ne hanyar kawai da za a kawo karshen yakin da suke da Rasha.

Tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a 2022, biranen kasar ke fama da lugudan wuta daga Rasha.

Hare-haren da Rashan ke kai wa Ukraine din sun lalata wurare da dama kama daga sansanin sojojin kasar da gidaje da makarantu da asibitoci da tashoshin lantarki da na makamashi da dai sauransu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ukraine ta ce rashin amince mata yin amfani da makami mai cin dogon zango a kan Rasha zai haifar mata da cikas.

Shugaban Zelensky, ya ce idan aka ba su izinin, a cikin ƴan watanni za su lalata na'urorin da ke harba makamai masu linzami na Rasha.

Da yake jawabi a birnin Kyiv, shugaba Zelensky ya ce Rasha ba za ta kawo ƙarshen mamayar da take wa Ukraine ba har sai ta kasa kare kanta.

A baya dai Burtaniya ta ce Ukraine na da damar amfani da makaman da ta bata don kare kanta, bayan da Ukraine ta kutsa iyakar Rasha a watan Augusta, to amma daga cikin makaman ban da mai cin dogon zango.

Amurka ta samar wa Ukraine irin wadannan makamai a farkon shekarar da muke ciki wato 2024, to amma sauran kasashen yamma kawayen Ukraine ba su bata damar amfani da su ba musamma a cikin Rasha.

Bayan tattaunawa akan Ukraine, shugabannin biyu wato Biden da Kier Starmer, sun kuma tattauna batun halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, inda yakin da ake a Gaza ya kusa cika shekara guda tare da dai-daita mutane da dama.