Kungiyar Kiristoci a Najeriya ta koka da yawan sace mambobinta

Coci
An wallafa

Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN, ta bayyana damuwarta a kan yawan sace limaman coci da masu binsu da ‘yan bindiga ke yi a jihar Kaduna da ma wasu sassa na kasar.

 

Shugaban kungiyar reshen jihar Kaduna Rabaran Joseph John Hayab, ya shaida wa BBC cewa, sace-sacen fada-fada da fastoci sai kara karuwa yake yi musamman a jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya.

 

Ya ce, ”A tunaninmu yakamata a ce na riga na shawo kan wannan matsala to amma har yanzu yi a ke.”

 

Rabaran Hayab, ya kuma ce, ”A yanzu haka a jihar Kaduna an saci fada-fada kusan 18 idan ma ba su kai ashirin ba a cikin shekaru uku da suka wuce.”

 

Ya kara da cewa an saci mambobi wanda ba zai iya fadin adadinsu ba, don yana ganin idan aka hada da yaran makaranta sauran Kiristocin da aka sata a kauyuka adadinsu zai kai wa dubbai.

 

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban na CAN, reshen jihar ta Kaduna, ya ce sam bai kamata ace ana irin wannan sace-sacen ba, saboda ana da gwamnati da jami’an tsaro.

 

Rabaran Hayab ya ce bai sani ba ko ‘yan bindigar da suke sace limaman coci na ganin ko suna da kudi ne, idan har haka suke tunani to sun yi kuskure:

 

‘’Duk wanda ya san aikin fada ko limamin coci, to ya san cewa aiki ne na sadaukar da kai ba wani kudi ake biyansu ba.’’

 

Kungiyar Kiristocin dai ta yi wannan martani ne bayan sace wasu limaman coci biyu da 'yan bindiga suka yi a jihar Kaduna.

 

Tuni dai Rundunar 'yan sandan Najeriyar ta ce tana kokarin kubutar da mutanen, inda kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna ya shaida wa BBC cewa jami’an na nan na kokarin kubutar da limaman cocin biyu na cocin Katolika.

 

Rahotanni sun ce an sace limaman cocin ne a yankin karamar hukumar Lere da ke Jihar ta Kaduna.

 

Kungiyar Kiristoci reshen jihar Kadunan, ta ce wadannan fada-fada da aka sace sun tafi gudanar da wani shiri ne a Lere a nan ne aka sace su.