Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Van de Beek, Ruiz, Bowen, Cantwell, Lookman, da Broja

Asalin hoton, PA Media
Manchester United ta tallata wa Newcastle da Borussia Dortmund dan wasan tsakiyarta Donny van de Beek. (Manchester Evening News)
A wata mai kama da haka United na kan gaba wurin neman sayen dan wasan tsakiyar Napoli da Sfaniya Fabian Ruiz. (La Republica - in Italian)
Hakama United din na shirin bai wa Marcus Rashford sabon kwantiragin a karshen kaka. (ESPN)
Kazalika har yanzu kungiyar na ci gaba da tattaunawa da kocin PSG Mauricio Pochettino. (Le Parisien - in French)
Ita kuwa Liverpool na shirin dauko dan wasan gaban West Ham ne wato Jarrod Bowen. (Football Insider)
A nan kuma Newcastle ce ke son sayen dan wasan tsakiyar Norwich da Ingila Todd Cantwell. (Rudy Galetti - Calciomercato)
Newcastle din har wayau ta nemi a sayar mata da mai tsaron bayan Sevilla Diego Carlos. (Sky Sports)
Tottenham kuwa na ci gaba da sauraren kungiyoyin da ke da sha'awar sayen dan wasanta na tsakiya Tungay Ndombele, kuma a na tunanin ya tafi Juventus. (Mirror)

Asalin hoton, Getty Images
Southampton kuwa na neman mayar da zaman Armando Broja a kungiyar na din-din-din daga Chelsea. (Sky Sports)
A Jamus kuwa Borussia Dortmund ta nuna sha'awar daukar mai staron bayan Chelsea da Denmark Andreas Christensen. (Patrick Berger - Sport1)
Idan muka sake lekawa Liverpool Jurgen Klopp na son dan wasan gabansa Divock Origi ya ci gaba da zama kungiyar har bayan watan Janairu. (Liverpool FC)
Kuma akwai jita-jita mai karfi da ke nuna cewa akwai yiwuwar Liverpool din ta kawo dan wasan tsakiyar Borussia Dortmund Jude Bellingham. (Caught Offside)
A London kuwa Arsenal ta ce mutum bakwai ta shirya kawowa ciki hadda Youri Tielemans na Leicester da kuma Georginio Wijnaldum na PSG. (Mirror)
A wata mai kama da haka kocin Leicestre Brendan Rodgers na son saye ademola Lookman na RB Leipzig da ke zaman aro a kungiyar. (Leicester Mercury)
A nan kuma Machester City ta nuna sha'awar dauko dan wasan tsakiyar Flamengo a Brazil Matheus Franca. (BolaVip - in Spanish)











