Antonio Rudiger: Rudiger zai ci gaba da wasa a Chelsea in ji Thomas Tuchel

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Chelsea, Thomas Tuchel ya ce yana da ''tabbacin'' cewar mai tsaron baya, Antonio Rudiger zai sa hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar.
Mai shekara 28 dan kwallon Jamus yana da damar tattaunawa da wasu kungiyoyin tun daga yanzu, bayan da kwantiraginsa zai kare a Stamford a karshen kakar 2021-22.
Rudiger ne ya ci kwallon da Chelsea ta doke Tottenham 1-0 a wasa na biyu a Caraboa Cup ta kuma kai zagayen karshe da ci 3-0 gida da waje.
Rudiger wanda ya buga wasan karshe a Champions League da Chelsea ta doke Manchester City 1-0, ana ta alakanta shi da zai koma ko dai Paris St-Germain ko Real Madrid ko Bayern Munich.
Ya kuma je Chelsea kan fam miliyan 29 daga Roma a Yulin 2017, wanda ya lashe FA Cup da Europa League da kuma European Super Cup a kungiyar ta Stamford Bridge.
Chelsea za ta buga wasan karshe da duk wadda ta yi nasara a wasan da za a buga ranar Alhamis tsakanin Liverpool ko Arsenal ranar 27 ga watan Fabrairu a Wembley.
Kungiyar Stamford Bridge tana ta biyu a teburin Premier League ta bana da tazarar maki 10 tsakaninta da Manchester City wadda ke jan ragama.
A makon jiya Tuchel ya ce ya yadda da dan wasa Rudiger, kuma baya ganin batun tsawaita yarjejeniyar dan kwallon a Chelsea da wata matsala.











