Karim Benzema ne fitatcen dan wasa a El Clasico a Spanish Super Cup

Asalin hoton, Getty Images
An bayyana Karim Benzema a matakin fitatcen dan wasa a karawar hamayya ta El Clasico tsakanin Real Madrid da Barcelona ranar Laraba.
Real Madrid ta kai wasan karshe a Spanish Super Cup, bayan da ta doke Real Madrid 3-2 a fafatawar da suka yi a Saudi Arabia.
Benzema dan wasan tawagar Faransa ya buga minti 120 a wasa da Barcelona, shine ya bai wa Vini Junior kwallon da ya fara ci, sannan da kansa ya zura na biyu a raga, daga baya Federico Valverde ya kara na uku a karin lokaci.
Wadanda suka ci wa Barcelona kwallaye sun hada da Luuk de Jong da kuma Ansu Fati.
Ranar Alhamis za a buga dayan wasan daf da karshe tsakanin Atletico Madrid da Athletic Bilbao, duk wadda ta yi nasara ta fuskaci Real Madrid a wasan karshe ranar 16 ga watan Janairu.
Real Madrid tana ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki biyar tsakaninta da Sevilla ta biyu mai maki 44.
Barcelona kuwa wadda ke ci gaba da fuskantar kalubale a bana tana ta shida mai maki 32 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.







