Yankin Tigray: Habasha ta yi barazanar zage ƙwanjinta a kan masu neman ɓallewa

Asalin hoton, AFP
Habasha ta yi gargadin cewa za ta iya tura ''dukkan karfin tsaronta'' kan yan tawayen yankin arewacin Tigray bayan nasarorin da suka samu kwanan nan.
Yan tawaye sun karbe ikon garin Lalibela, cibiyar hukumar adana kayan tarihi ta Unesco da ke makwabtaka da yankin Amhara, ranar Alhamis.
Gwamnati ta ce idan mayakan suka ci gaba da amfani da damar da ta bayar ta shigar da jin kai, to ita ma za ta zage dukkan kwanjinta ta tunkare su gaba gadi.
Fada ya yi kamari tsakanin bangarorin biyu tun watan Yuni lokacin da 'yan tawayen, wadanda suka hada da kungiyar' yan fafutukar neman 'yanci ta Tigray (TPLF) da kawayenta, suka sake kwace yawancin yankin Tigray a wani farmaki.
Sojojin kasa sun janye tare da ayyana tsagaita wuta na bai daya.
An toshe hanyoyin ba da agaji zuwa Tigray kuma hukumomi suna tattara mayaƙa, tare da yin taruka don duba yadda za a tunkari lamari.
'Yan tawayen na son a sasanta rikicin ta hanyar tattaunawa, amma ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce abin da suka yi ba shi da wata ma;ana.
Gwamnatin Habasha ta ayyana TPLF a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda, amma kuma ƴan tawayen sun ce ƙungiyar ita ce halattaciyar jam'iyyar yankin.
TPLF ta dawo daga rakiyar Firaiministan Habasha kan sauye-sauyensa na siyasa, ko da yake ta ƙwace sansanonin soji a Tigray da suka yi tasiri ga farmakin watan Nuwamba.











