Saƙon Shugaba Buhari na Babbar Sallah ga ƴan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na samar da ƙasa mai adalci, daidaito da ci gaba wacce za a tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Shugaban ya bayyana haka ne a cikin sakonsa na murnar zagayowar ranar Babbar Sallah da Musulmai ke bikinta a faɗin duniya.
A wata sanarwa mai ɗauke da saƙon, Shugaba Buhari ya yi magana a kan kalubalen da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu, inda ya ce "annobar korona ta yi matukar illa ga tattalin arzikin dukkan kasashe, ciki har da Najeriya, baya ga yadda ambaliyar ruwa ta haifar da mummunar barna ga gonaki.
"Hakan ya kawo naƙasu ga ƙoƙarinmu na bunkasa noman cikin gida daidai da tsarinmu na rage shigo da abinci daga ƙasashen waje," in ji Shugaba Buhari.
Ya kuma ce wannan ya haifar da hauhawar farashin abinci wanda gwamnati ke aiki tuƙuru don magancewa.
"A matsayina na zaɓaɓɓen shugaban kasa wanda yake da farin jinin talakawan da suka zaɓe mu, bari na tabbatar muku cewa muna ci gaba da daukar matakan kawo sauƙi ga 'yan Najeriya.
"Ciki har da samar da takin zamani a kan farashi mai sauƙi ga manomanmu," in ji shi.
Shugaba Buhari ya kuma yi magana a kan rashin tsaro da ake fama da shi a halin yanzu a kasar da ya ce ya haifar da mummunar illa ga harkar noma, saboda 'yan fashi da ƴan ta'adda sun hana manoma shiga gonakinsu.
"Bari in kuma yi amfani da wannan damar don in tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa muna daukar matakai don magance kalubalen tsaro da muke fuskanta.
"Mun fara karbar jiragen saman yaƙi da sauran kayan aikin soja da kayan aiki masu muhimmanci don inganta ƙarfin jami'an tsaronmu na tunkarar ta'addanci da ƴan fashi," in ji shi.
Da yake magana kan mahimmancin bikin Babbar Sallah, Shugaban ya yi kira ga Musulmai "da su nuna kyawawan halaye na Musulunci ta hanyar misalai da halaye na ƙashin kai.
"Amfani da bikin don cin gajiyar ƴan kasa ta hanyar tsauwala farashin kayan abinci da raguna ya saɓawa kyawawan halaye na addinin Musulunci.










