Majalisar dattawan Amurka ta karɓi daftarin tsige Trump

Asalin hoton, Getty Images
Yan jam'iyyar Democrats a Majalisar Wakilan Amurka sun gabatar da daftarin tsige tsohon shugaban kasar Donald Trump ga Majalisar Dattawa.
Daftarin ya kunshi tuhuma guda da ake yi wa shugaban ta yi wa magoya bayansa angiza mai kantu wajen afkawa Majalisar a farkon wannan watan.
Sai a watan Fabrairu ne majalisar za ta fara sauraron shari'ar da za a yi wa tsohon shugaban, don bawa Shugaba mai ci Joe Biden damar mayar da hankali kan ajandarsa.
'Yan majalisar dattijan na Democrats na buƙatar' yan Republican goma sha bakwai don kama Trump da laifi, wanda hakan zai hana shi sake rike wani mukami na gwamnati, ko ma sake tsayawa takara har abada.
Daruruwan magoya bayansa ne suka suka kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin kasar da ke Washington a daidai lokacin da 'yan majalisar ke yunkurin tabbatar da nasarar zababben shugaban kasar Joe Biden.
Hargitsin ya haifar da mutuwar farar hula 4 da jami'in dansanda 1.
Wannan mamaye da aka yi wa majalisar ya zo ne jim kadan bayan Trump ya yi jawabi ga magoya bayansa, inda ya ce "Ba za mu saduda ba, ba za mu amince da shan kaye ba."
Wasu ƴan jam'iyyar Republican dai na suka a kan cewa kamata ya yi a ƙyale shugaban ya sarara tunda dai an miƙa mulki cikin kwanciyar hankali.
A nasu ɓangaren yan jam'iyyar Democrat na ganin cewa dole ne a tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, ta yadda irin haka ba za ta sake faruwa ba a nan gaba.











