Rikicin Libya na son cin ministan harkokin cikin gida

Libya has been riven by violence since Col Muammar Gaddafi was deposed in 2011

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun 2011 Libya ta fada cikin rikici
An wallafa

Gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ke mara wa baya a Libya ta dakatar da ministan harkokin cikin gida tana tuhumarsa da rashin iya aiki bayan da wata zanga-zangar da aka yi cikin makon nan ta tayar da hakula.

A baya, minista Fathi Bashagha wanda yana da karfin fada-a-ji a birnin Misrata mai tashar jirgin ruwa, ya yi alkawarin daukar mataki kan sojoji 'yan sa kai da suka rika yin harbin mai uwa da wabi kan masu zanga-zangar a birnin Trabulus saboda matsin tattalin arziki.

Duk da cewa babbar matsala da ke damun Libya ita ce ta rikicin iko da ke tsakanin gwamnatin da MDD ke mara wa baya da kuma dakarun Janar Khalifa Haftar, (wanda yayi yunkurin kwace babban birnin amma ya gaza), akwai kuma wasu matsalolin cikin gwamnatin, musamman tsakanin bangarori biyu da suka fito daga Misrata da na Trabulus.

Dakatar da ministan harkokin cikin gida Fathi Bashaga ya bayyana boro-boro girman wannan matsalar.

A 'yan kwanankin da suka gabata mazauna birnin trabulus sun gudanar da zanga-zanga saboda karuwar matsin tattalin arziki da ta addabe su, kuma sun bukaci firaminista Fayez Sarraj ya ajiye mukaminsa.

Ministan harkokin cikin gidan yayi tir da sojojin sa kan, saboda kai harin da suka yi kan masu zanga-zangar har suka rika sace wasu daga cikinsu.

An dai dakatar da shi daga mukaminsa kuma za a gudanar da bincike kan ayyukansa.

Libya ta shafe shekara tara cikin kazamin rikici tun bayan da wasu kasashen yamma karkashin jagorancin hukumar tsaro ta NATO ta hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Muammar Gaddafi.