Trump ya dauki kwararrun lauyoyi domin kare shi

A mako mai zuwa ne za'a fara sauraren kara a sabon zaman da za a gudanar.
Bayanan hoto, A mako mai zuwa ne za'a fara sauraren kara a sabon zaman da za a gudanar
An wallafa

Shugaban Amurka Donald Trump ya dauko kwararrun lauyoyi da za su kare shi a gaban majalisar dattawa.

Ken Starr da Robert Ray da su ka yi shari'ar tsohon shugaba Bill Clinton, da kuma Alan Dershowitz da ya kare dan jaridan nan da a ka zarga da kashe matarsa a shekarar 1995 OJ Simpson na daga cikin masu kariyar shugaban.

Fadar White House ta sanar da cewa babban lauyan Mr Trump Pat Cipollone ne zai jagoranci tawagar.

A mako mai zuwa ne za a fara sauraren kara a sabon zaman da za a gudanar.

Masana sun ce lauyoyin da za su wakilci shugaban sun shahara sosai, musamman Mr Starr wanda ya gudanar da bincike lokacin da a ka zargi tsohon shugaba Bill Clinton da alaka da Monica Lewinsky, wata matashiya da ke sanin makamar aiki a fadar White House a lokacin mulkinsa.

Ken Starr da Robert Ray ne su ka yi shariar tsohon shugaba Bill Clinton

Asalin hoton, Reuters da Getty Images

Bayanan hoto, Ken Starr da Robert Ray ne su ka yi shariar tsohon shugaba Bill Clinton

Binciken ya sa majalisar wakilai ta tsige Mr Clinton a shekarar 1998.To amma daga baya sai majalisar dattawa ta wanke shi.

A hirarsa da gidan talabijin na CBS, daya daga cikin lauyoyin Alan Dershowitz ya ce shi ba dan siyasa bane, kuma aikin da zai yi ba shi da alaka da siyasa.

A cewarsa abune da ya shafi kundin tsarin mulki a kan haka ya na da natsuwa kan aikin da zai yi.

Mr Dershowitz ya ce ya damu matuka irin yadda ake son amfani da siyasa don tsige Mr Trump, inda yace hakan tamkar bude kofa ne ga 'yan siyasar da ke son anfani da son zuciya wurin cimma burinsu.

Lauyan ya ce ko a baya bai aminta da tsige Mr Clinton ba, kuma Hillary Clinton ya jefa wa kuri'a a zaben 2016.

Ko a lokacin binciken katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Amurka Shugaba Trump ya nemi shawarar Mr Dershowitz.

To sai dai wata majiya na cewa an samu rabuwar kai a fadar White House kan saka sunan shararren lauyan a cikin tawagar da za ta kare Mr Trump, ganin irin alakarsa da wasu da fadar ba ta ga maciji da su ba.