Premier League: Everton ta sallami kocinta Marco Silva

Tsohon kocin Everton Marco Silva

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Silva ya ce matsin lamba ce ta janyo rashin katabus din da 'yan wasan Everton ke yi
An wallafa

Everton to kori kocinta Marco Silva bayan wata 18 da ya shafe a matsayin kocinta.Wannan na zuwa ne biyo bayan shan kashin da kungiyar ta yi a wasan hamayya tsakaninta da Liverpool da ci 5-2.Rashin nasarar a jiya Laraba a filin wasa na Anfield shi ne karo na tara da kungiyar ta yi, lamarin da ya sanya ta koma matsayi na 18 a teburin Premier.Silva, wanda ya karbi ragamar kungiyar a watan Mayun 2018, ya samu nasara a wasa 24 ya kuma yi rashin nasara sau 24 a cikin wasa 60 da ya jagoranci kungiyar.Tsohon dan wasan bayan kungiyar Duncan Ferguson ne yanzu haka zai ci gaba da rikon kungiyar na wucin gadi, inda zai jagorance ta a wasan da za su fafata da Chelsea ranar Asabar.Tun farko kulob din da ma ya ce yana da niyyar nada sabon koci cikin hanzari.Yanzu Everton na yunkurin nada koci na hudu na dindindin tun bayan da ta kori Roberto Martinez a watan Mayun 2016.

Ana sa ran tsohon kocinta David Moyes a matsayin wanda zai karbi aikin na wucin gadi. Sai dai magoya baya sun nuna rashin amincewarsu da daukar Moyes.