Club World Cup: Liverpool ta fitar da sunan 'yan tawagarta

Tawagar liverpool

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Liverpool ta casa Arsenal 5-4 a bugun finariti a zagaye na 4 na gasar Carabao bayan sun yi canjaras 5-5
An wallafa

Liverpool ta fitar da sunayen 'yan wasa 23 da za su buga gasar Kofin Duniya na kulob-kulob wato Fifa Club World Cup, wanda zai ci karo da wasan Carabao Cup da za ta buga da Aston Villa.

18 daga cikin 'yan wasa 19 da aka ambata sun fafata a gasar Premier a makon da ya gabata , inda yanzu haka za su yi tattaki zuwa kasar Qatar.

Daga cikin 'yan wasan akwai Rhian Brewster da Curtis da Jones da Harvey Elliott da Neco Williams.

Hakan dai na nufin 'yan wasan ba za su buga wasanta da Villa ba.

'Yan wasan Jurgen Klopp za su fafata a Villa ranar 17 ga Disamba da karfe 7:45 agogon Najeriya sannan su fafata a wasan kwata fayinal a gasar Fifa Club World Cup a kasar Qatar washegari da karfe 5:30.

Liverpool ta ce ta dauki matakin yin amfani da tawaga biyu ne saboda ba a ba a tsara wasannin ba yadda "za su dace da wasannin Premier da kuma bai wa 'yan wasanta damar samun hutu".

Mai tsaron raga Caoimhin Kelleher, wanda aka ajiye a benci a wasan da Liverpool ta doke Everton da ci 5-2 ranar Laraba, ba ya cikin tawagar da za su wakilci kungiyar.

Andy Lonergan na cikin masu tsaron ragar da za su je wasan a Qatar ciki har da Alisson da Adrian.

Dan wasan baya Joel Matip da dan wasan tsakiya Fabinho suna jinyar rauni, hakan na nufin ba sa cikin tawagar.

Tawagar da za ta je Qatar:

'Yan wasan Liverpool da suka fito a tawagar da za ta fafata a wasa biyu na gasar ta Fifa Club World Cup sun hada da:

Alisson, Van Dijk, Wijnaldum, Lovren, Milner, Keita, Firmino, Mane, Salah, Gomez, Adrian, Henderson, Oxlade-Chamberlain, Lallana, Lonergan, Shaqiri, Brewster, Robertson, Origi, Jones, Alexander-Arnold, Elliott, Williams.