Wakilin Bale ya ce ba lallai ya bar kulob din ba

Asalin hoton, Reuters
Wakilin dan wasan Real Madrid Gareth Bale wato Jonathan Barnett ya ce dan wasan ba ya cikin annashuwa sosai a Madrid amma duk da hakan babu tabbacin zai bar kulob din a watan Janairu.
Dan wasan gaban Wales, mai shekara 30, ya dauki Kofin Zakarun Turai na Champions League sau hudu cikin shekara shida tare da Real Madrid, kodayake saura kiris ya rage masa ya koma kulob din Jiangsu Suning na kasar China.
"Ba a bukace shi ya bar kulob din ba har yanzu," in ji Barnett.
"Yana da kwantaraginsa da Real Madrid kuma muddin suna son sa, babu abin da kowa zai iya yi."
Bale ya koma Real Madrid daga Tottenham a kan kudi fan miliyan 85 a watan Satumbar 2013 kuma ya taimaka mata lashe gasar kofin duniya ta Club World Cup da Uefa Super Cup guda uku da La Liga daya da Copa del Rey daya, da kuma Gasar Champions League.
Amma a watan Yuli an tsara zai koma China bisa kwantiragin shekara uku, inda aka yi tsammanin zai rika karbar albashi fan miliyan daya a kowanne mako, kafin yarjejeniyar ta rushe lokacin da Real ta bukaci a biya ta diyya.
A lokacin, kocin Real Madrid Zidane ya ce ficewar ta Bale "za ta fi dacewa ga kowa", kuma tun daga lokacin ne dan wasan ke ci gaba da fuskantar kalubale daga magoya bayan Madrid musamman yadda suka rika yi masa ihu a wasansu da Real Sociedad a watan jiya.
Da aka tambaye shi ko Bale yana jin dadin zama a kulob din, Barnett ya ce: "Ba ya jin dadi gaskiya.
"Yana da kwantaragin da ya sanya hannu a kai kuma muddin ya kasance dan wasan Real Madrid zai taka-leda dari bisa dari - kuma ya bayar da gudummawa sosai. Yana son lashe Champions League.
"A bayyane take cewa idan har yana fili lokacin da Madrid ke wasa tana da damar lashe wasan.
"Babu wanda ya taba sukar sa cewa baya bayar da gudummawa 100%. Gareth Bale yana daya daga cikin fitattun 'yan wasa a duniya. Ya kamata kocin ya yi murna kasancewar yana tare da shi a fili.
"Ba mu da tabbas ko zai tafi. Idan dama ta zo masa kuma abu ne da yake so ya yi, dole ne mu tattauna da shugaban Real Madrid kan makomar da halin da ake ciki."









