Ruwa ya yi barna a biranen India

An wallafa

Sama da mutane 100 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a arewacin India sakamakon tunbatsar da kogin Ganga ya yi.

An sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin Bihar da Uttar Pradesh, ya yin da masu aikin ceto sukai nasarar kwashe dubban mazauna yankin.

Ambaliyar ruwan ta daidaita birnin Patna mai mutane miliyan biyan biyu. Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya kusa shafe motoci.

Tashoshin jirgin kasa, da mota, da asibitoci da makarantu duk ambaliyar ta shafa. Ya yin da aka samu katsewar wutar lantarki a Patna da Uttar Pradesh.

Haka kuma ruwan ya shafi gidan Kurkuku, lamarin da ya sanya dole hukumomi suka kwashe sama da fursunoni 500 daga gundumar Ballia sakamakon shanye gine-gine uku da ruwan ya yi.

A baya dai ruwa na janyewa a watan Satumba a kasar India, amma yanzu masu hasashen yanayi sun damunar ba na ta musamman ce da aka dade ba a gani ba cikin shekaru 50.