'An fi kashe mutane a Afghanistan kan Syria da Yemen gaba daya'

Asalin hoton, Others
Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewa adadin fararen hula da suka mutu a rikicin Afghanistan a watan da ya wuce na Agusta ya fi wadanda suka hallaka a Syria da Yemen idan aka hada.
Mutum 2,300 ne aka kashe a kasar cikin watan Agustan, daga cikin su kuma guda 473 fararen hula ne, yayin da sauran kuma ko dai mayakan Taliban ne ko kuma jami'an tsaro, kamar yadda binciken ya nuna.
A kididdigar da binciken ya nuna, ana hallaka akalla maza manya 74, mata da kananan yara su ma a kullum sai an kashe a kasar ta Afghanistan a kowace rana ta watan na Agusta da ya gabata, kamar yadda binciken na BBC ya gano.
Rahoton ya nuna yadda rikicin wanda ba a kakkautawa ya shafi kusan dukkanin kasar baki daya yayin da tattaunawar Amurka da 'yan Taliban, kan ficewar sojojin Amurkar bayan shekara 18 ta yaki ta wargaje, ko da yake ba a yanke kauna ta komawa kan tattaunawar ba.

Asalin hoton, Others
BBC ta tabbatar a binciken lamuran da suka danganci tsaro na hadari ko wani lamari wadanda mutane dubu biyu da 307 suka mutu.
A tsawon watan Agustan, kusan mayakan Taliban da jamian tsaro 1,800 suka mutu.
Sai dai kuma dukkanin bangarorin biyu, na Taliban da kuma na gwamnatin Afghanistan sun nuna shakku ko kin amincewa da alkaluman yawan mace-macen da BBC ta fitar.
Duk da musu ko tababar da bangarorin suke nunawa a kai, sakamakon binciken ya zo daya da wani nazari na majalisar dinkin duniya, wanda ya nuna cewa yawan fararen hula da dakarun gwamnati suka kashe ya fi wadanda kungiyar Taliban ta hallaka.

Haka kuma rahoton na BBC ya kara nuna cewa yawancin wadanda suka rasa rayukan nasu a wannan lokaci a kasar, mayaka ne, wadanda daga cikinsu na Taliban sun zarta yadda aka yi tsammani, amma dai kashi daya bisa biyar na adadin farar hula ne.
Bayan wadanda aka hallaka, akwai kuma wasu karin 1,948 wadanda su kuma aka jikkata a watan na Agusta.
Alkaluman wadanda rayukan nasu suka salwanta da wadanda suka jikkatan, 'yar alama ce kawai ta halin da ake ciki a Afghanistan din.
Wadda kuma ke nuna yadda al'amura za su iya kara tabarbarewa a gaba, yayin da Shugaba Trump ke neman tabbatar da wata muhimmiyar manufa ta harkokin wajen kasarsa, ya janye sojojin kasar daga Afghanistan.

Asalin hoton, Others
A halin da ake ciki dai babu wani batu na wata alama ta dakatar da bude wuta da kai hare-hare da ake shirin yi, kuma daruruwan 'yan kasar ta Afghanistan na mutuwa a rikicin kowane mako ko ma rana.
Bugu da kari akwai ma fargabar karuwa da tabarbarewar tashin hankalin kafin zaben shugaban kasar da za a yi a karshen watan nan.










