Za a yi macin miliyoyin mutane a Algeria

Wasu lauyoyi masu zanga-zanga a Algiers

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Masu zanga zanga a Algeria sun bukaci jama'a su fito yau Juma'a domin yin zanga-zangar da aba a taba ganin irinta ba a kasar.

Wadanda suka shirya wannan zanga-zangar na son hana shugaba Abdulaziz Bouteflika ya tsawaita wa'adin mulkinsa ne.

Tun dai watan jiya 'yan kasar suka fara nuna ranshin amincewarsu da matakin da shugaban mai shekara 82 da haihuwa ke son dauka.

Wadanda suka kira jama'a su fita titunan kasar suna kiran wannan Macin Mutum Miliyan Ashirin: wanda wani take ne da masu adawa da mulkin Shugaba Bouteflika ke amfani da shi na hana shi sake tsayawa takara bayan ya shafe shekara 20 yana mulkin kasar.

Rabon da a ga shugaba a bainar jama'a tun 2013.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rabon da a ga shugaba a bainar jama'a tun 2013

Rabon da a ga shugaba a bainar jama'a tun 2013, kuma a halin yanzu yana jinya ne a wani asibiti da ke birnin Geneva na kasar Switzerland.

Amma duka da bacin ran da ake nunawa, shugaban ya sanar da 'yan kasar cewa lallai zai sake tsaywa takara, kuma ya yi alkawarin shirya wani babban taron kasa tare da yin alkaarin sauka daga mukaminsa bayan shekara daya idan an sake zaben shi.

Wannan matakin ya kara fusata mutanen kasar da ke ganin Mista Bouteflikan ba shi da lafiyar da zai iya sauke nauyin shugaban kasa.

Amma masu neman sauyi a kasar na fuskantar tarjiya daga wadanda ke amfana da mulkin, kuma kawo yanzu hankalin jama'a na kan sojojin kasar wadanda kawo yanzu ba su dauki wani mataki ba.

Idan suka juya wa gwamnatin kasar baya, to babu makawa gwamnati mai ci da 'yan Algeriya suka lakaba wa suna 'le pouvoir' - wata karfin mulki ta zo karshe kenan.