Ghana: 'Za mu yi maganin 'yan fashi da makami'

Shugaban kasar Ghana ya tattauna da gaggan masana harkokin tsaro na kasa dangane da yadda za`a shawo kan fashi da makami da yayi tsamari a baya bayan nan a wasu sassa na Ghana.
Shugaban ya takaita kwanakin da zai yi Amurka ne, inda ya juyo gida bayan da al`ummar kasar Ghana suka nuna matukar damuwa dangane da yawaitar fashi da makami a baya bayan nan.
Wasu 'yan kasar sun ce su na zaman zullumi ne, da gudanar da harkokin kasuwanci cikin kasada saboda barayi na addabar su.
A kwanakin baya wasu 'yan fashi da makami sun kai hari wani kamfani da rana tsaka, sukai awon gaba da kudin da suka kai CD 500,000, kwatankwacin dalar Amurka 110,000.
Sannan wasu 'yan bindiga sun kai hari ofishin 'Yan sanda a kasar inda suka kubutar da wasu 'yan uwansu guda bakwai da 'yan sandan ke tsare da su.
'Yan bindigar sun abka ne hedikwatar 'yan sanda a gundumar Kwabaye da ke Accra da safiyar Lahadi.
Rahotanni sun ce 'yan fashin sun raunana jami'in 'yan sanda, a lokacin da suka kai harin, kuma daga bisani jami'in ya rasu.
'Yan fashin da suka tsere sun kunshi 'yan Ghana shida da wani dan Najeriya daya.
Gwamnati ta yi alkawarin kara yawan jami'an tsaro, da na sintiri da za su gudanar da ayyukansu babu dare babu rana, dan tabbatar da tsaro.











