Real Madrid ta dauki Champions da La Liga da Spanish Super Cup a bana

Asalin hoton, Real Maddrid FC
Real Madrid ta karkare kakar tamaula ta 2021/22 da lashe Champions League da La Liga da kuma Spanish Super Cup.
Ranar Asabar Real Madrid ta doke Liverpool 1-0 ta dauki Champions League na kakar nan, kuma na 14 jumulla.
Tun kafin nan kungiyar ta Santiago Bernabeu ta fara da cin Spanish Cup na 12 jumulla, sannan ta dauki La Liga na 35.
Champions League na 14 jumulla
Real karkashin Carlo Ancelotti ta doke fitattun kungiyoyi a Turai kafin ta dauki babban kofin Zakarun Turai na kakar nan, kuma na 14 jumulla.
Cikin wadanda ta doke sun hada da Paris St Germain da Chelsea da Manchester City da kuma Liverpool a wasan karshe a birnin Paris din Faransa.
Thibaut Courtois ne ya lahe kyautar dan wasan da yafi taka rawar gani a karawar ta karshe a ranar Asabar.
La Liga na 35 jumulla
Real Madrid ta yi nasarar lashe La Liga na bana a ranar 30 ga watan Afirilun 2022, bayan da ta doke Espanyol a Santiago Bernabeu, saura wasa hudu a kakarkare gasar.
Kungiyar ta doke manyan kungiyoyi a La Liga ciki har da Barcelona a Camp Nou da Sevilla da Atletico Madrid a Bernabeu.
Benzema ne ya lashe kyautar dan wasan da yake kan gaba a zura kwallaye a raga a La Liga ta kakar nan mai 27 a raga, sai Vinicius Jr. mai 17 ya kuma bayar da 10 a ka zura a raga.
Spanish Super Cup na 12 Jumulla
Ranar 16 ga watan Janairun 2022 Real Madrid ta dauki Spanish Super Cup na bana kuma na 12 jumulla.
Real ta lashe kofin a birnin a Riyadh, Saudi Arabia, bayan da ta doke Barcelona 3-2 a karawar daf da karshe, sannan ta ci Ahletic Bilbao 2-0 a wasan karshe.
Dan wasan Real Madrid, Luca Modric shi ne gwarzon dan wasa a gasar.
Tarihin da aka kafa
Kyaftin din Real Madrid, Marcelo ya zama dan wasan Real Madrid wanda ke kan gaba a daukar kofuna a kungiyar mai 25 jumulla.
Carlo Ancelooti ya zama na farko da ya lashe Champions League hudu, biyu a Real Madrid da biyu a AC Milan - haka kuma shi ne da ya dauki kofi biyar a manyan gasar Turai fitattu biyar.
Benzema ya zura kwallo 44 a kakar bana, shi ne kan gaba a cin kwallaye a La Liga da kuma Champions League.









