Newcastle za ta dau Kane, Leeds ta tuntubi Bruno Fernandez

Watakila Newcastle United za ta tanadi fam miliyan 190 a watan Janairu domin sayen dan wasan Tottenham, Harry Kane da Kylian Mbappe, na Paris St Germain. (Telegraph - subscription required)
Watakila tsohon kocin Chelsea, Antonio Conte, ya maye gurbin Steve Bruce a matakin mai horar da Newcastle. (Sun)
Watakila dan wasan Brazil, Philippe Coutinho, mai shekara 29, ya koma taka leda a St James Park daga Barcelona a watan Janairu. (Sport - in Spanish)
Leeds United ta tuntubi dan wasan Manchester United, Bruno Fernandes, da kuma dan kwallon Brazil, Raphinha, mai shekara 24 kan batun komawa Elland Road da murza leda. Manchester United. (Mirror)
An yi wa tsohon dan kwallon Newcastle United, Demba Ba, mai shekara 36 tayin dawowa buga wa kungiyar tamaula, bayan da ya yi ritaya. (Star)
Dan wasan tawagar Jamus, Antonio Rudiger, shi ne na farko da take son dauka a badi, bayan da yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar bana. (ABC, via Mail)
Barcelona na son daukar matasa masu buga wasa daga tsakiya a watan Janairu ta kuma hangi dan kwallon Manchester United, Donny van de Beek da na Tottenham, Tanguy Ndombele, wadanda suka dace da ita. (Sport - in Spanish)
Ole Gunnar Solskjaer ba zai taba barin Van de Beek ya bar Manchester United a watan Janairu ba, zai kuma yi duk yadda ya kamata domin hana wata kungiya ta dauke shi. (ESPN)
Watakila Ainsley Maitland-Niles da kuma Mohamed Elneny, za su nemi izinin barin Arsenal a watan Janairu, domin komawa wata kungiyar da za ta ke saka su a wasa da yawa. (Sun)
Dan wasan Argentina Sergio Aguero, bai yadda ya koma Juventus ba, kafin ya amince da zuwa Barcelona, bayan da kwantiraginsa ta kare a bana a Manchester City kan fara kakar bana. (Sport - in Spanish)
Juventus na duba yadda za ta sayar da Aaron Ramsey a watan Janairu, bayan da West Ham da kuma Everton ke muradin daukar dan wasan. (Calcio Mercato - in Italian)









