Ko Karim Benzema zai lashe kyautar Ballon d'Or ta bana?

Asalin hoton, Getty Images
Karim Benzema ya lashe La Liga da Champions League a kakar 2021/22, ya kuma ci kwallo 44 a wasa 46 - shin ko zai iya daukar kyautar Ballon d'Or a bana kuwa?
Mai shekara 34, zai zama mai yawan shekarun haihuwa idan ya lashe kyautar bana, bayan dan kwallon Blackpool, Stanley Matthews, wanda ya zama zakara a 1956.
Mai tsaron ragar Real Madrid, Thibaut Courtois shi ne ya lashe kyautar dan wasan da yafi taka rawar gani a ranar Asabar a Faransa.
Haka kuma Vinicius Jr ne ya ci kwallon da Real ta doke Liverpool 1-0 da ta dauki kofi na 14 jumulla.
Benzema ya taka rawar gani a karawar, har da cin kwallo amma ba a karba ba.
Wasu na ganin dan wasan tawagar Faransa, ya cancanci ya lashe Ballon d'Or ta kakar nan da za a bikin bayar da kyautar ranar 17 ga watan Oktoba - ana ganin ba kamarsa a Turai a kakar nan.
Bayan da Real Madrid ta lashe La Liga da Champions League, Benzema ne kan gaba a cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da kuma ta Zakarun Turai ta kakar nan.
Ya zura kwallo 27 a La ligar nan da tazarar tara tsakaninsa da na biyu, sannan ya ci 15 a Champions League, kenan duk minti 74 ya ci.
Benzema ya zura 10 a raga daga zagaye na biyu a 15 din da ya ci a Champions League a bana.
Dan wasan ya kuma zura uku rigis a raga a karawa da Paris St-Germain da Chelsea, kuma shi ne ya ci Manchester City ta karshen da ya kai Real Madrid wasan karshe.









