Ralf Rangnick ba zai karbi aikin tuntuba a Manchester United ba

An wallafa

Tsohon kociyan rikon kwarya, Ralf Rangnick ba zai karbi aikin tuntuba na kaka biyu a Manchester United ba.

Maimakon hakan zai mayar da hankalinsa waje daya a sabon aikin horar da tawagar Austria.

Tun farko Rangnick ya amince da aikin tuntuba tun bayan da ya karbi kocin rikon kwarya a Manchester United cikin Disamba, bayan da ya maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer.

United wadda ta karkare kakar Premier League a bana a mataki na shida, za ta buga Europa League a badi, ta dauki Erik ten Hag daga Ajax domin ya fara aiki da wuri don tunkarar kakar gaba.

Rangnick ya tabbatar da kin karbar aikin tuntuba a Manchester United ranar Lahadi, a lokacin da yake ganawa da 'yan jarida, bayan da aka gabatar da shi mai horar da Austria.

Tun farko Rangnick ya karbi aikin kocin rikon kwarya a United zuwa karshen kakar bana, daga nan ya ci gaba da na tuntuba kaka biyu, tun bayan da aka sallami Solkjaer.

Rangnick ya ci wasa kaso 38 cikin 100, shi ne kocin da ya samu kaso mara yawa a jerin wadanda suka ja ragamar United a Premier League, rashin kokari kuma mafi muni a kungiyar tun bayan shekara 50.