Abu 5 da ke janyo rashin yarda tsakanin ma'aurata ko masoya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Rashin yarda shi ne rasa amana da dogaro a dangantaka, wanda kan sa zaman tare ya zama cike da rikice-rikice ko damuwa wanda kuma daga bisani ka iya janyo rabuwa.

Wani yanayi ne da ɗaya ko dukkan ɓangarorin biyu ba sa amincewa ko dogaro da juna gaba ɗaya.

Misali, Miji bai yarda da matarsa ba idan ta fita ko kuma matar ba ta yarda da mijin nata ba. Haka kuma tsakanin saurayi da budurwa ma mace tana zargin saurayinta da cin amana ko kuma saurayin na zargin budurwar tasa.

Abin tambaya a nan shi ne me ke janyo irin wannan rashin yarda da ka iya raba aure ko kuma zaman tare.

BBC ta tattauna da Maryam Hassan Baba, ƙwararriya kan inganta zamantakewar iyali, kuma mai shafin The Northern Therapist a Instagram.

Dalilan da ke janyo rashin yarda

Ƙwararriyar ta lissafa wasu dalilai guda biyar da ta ce su ne ke janyo rashin yarda tsakanin abokan zama:

  • Rashin ingantacciyar sadarwa: A mafiya yawancin lokaci rashin sanin yadda za a isar da saƙo a tsakanin ma'aurata ko kuma saurayi da budurwa musamman a lokacin da aka samu ɗan saɓani. Idan ba a faɗin gaskiya ko ba a bayyana ra'ayi yadda ya kamata ko kuma ɓoye damuwa ko jin haushi maimakon tattaunawa.
  • Karya alƙawari: Rashin cika alƙawari da yaudara da cin amana kan taimaka wajen kawar da yarda tsakanin abokan zama.
  • Ƙarya akai‑akai: Kasancewar ba a rana ɗaya rashin yadda ke shiga tsakanin abokan zama ba, yawan yin ƙarya akai-akai musamman ɓoye wasu muhimman abubuwa ga aboki ko abokiyar zama na janyo rashin yarda.
  • Kishi da shakku: Yawan kishi kan haifar da tsoron rasa abokin zama da zargi ba tare da hujja ba ga aboki ko abokiyar zama na janyo rashin yarda tsakanin ma'aurata ko kuma abokan zama.
  • Rashin mutunta juna: Cin mutunci, zagi ko raini da rashin daraja ra'ayin aboki ko abokiyar zama na daga cikin dalilan da ke janyo rashin yarda.

Hanyoyin gyara alaƙa

Maryam Hassan Baba, ƙwararriya kan inganta zamantakewar iyali, kuma mai shafin The Northern Therapist a Instagram ta kuma zayyana hanyoyi huɗu na gyara alaƙa a lokacin da ta yi tsami:

  • Tattaunawa cikin natsuwa tare da gaskiya
  • Gina amana ta hanyar gaskiya da cika alkawari
  • Mutunta juna a kowane lokaci
  • Neman shawarwari idan matsalar ta yi tsanani

Kalamai 6 da ba su dace ma'aurata su faɗa wa juna ba

Mutane da dama kan yi amfani da wani salo na nuna wa abokin hulɗarsu cewa akwai matsala a tunaninsu. Sai dai akasari sukan yi hakan ne domi neman wani abu a wurin ɗaya ɓangaren.

Mutane da dama kan yi amfani da wani salo na nuna wa abokin hulɗarsu cewa akwai matsala a tunaninsu. Sai dai akasari sukan yi hakan ne domi neman wani abu a wurin ɗaya ɓangaren.

Ƙwararriyar ta lissafa hanyoyi guda 6 kamar haka:

  • Mahaukaci/Mahaukaciya
  • Wasa nake yi
  • Kai ka jawo na aikata haka/Laifinka/ki ne
  • Idan kana so za ka iya yin haka/bari na kawai
  • Kowa ya yarda da ni ban da kai/ke
  • Kai/Ke ce babbar matsalar