Oman ta ƙiƙiri hanyar wucewar jiragen ruwa na wucin gadi a mashigar Hormuz
Oman ta sanar a ranar Talata cewa ta ƙirƙiri wata hanya na wucin gadi a teku domin sauƙaƙa zirga‑zirgar jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigar Hormuz.
Hakan ya biyo bayan haɗin gwiwa da Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Duniya (IMO) domin tabbatar da tsaro a wannan muhimmiyar hanya ta ruwa.
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Oman ya bayyana cewa duk jiragen da ke son wucewa ta mashigar dole ne su bi ƙa’idojin da aka gindaya, tare da yin hulɗa kai tsaye da hukumomin Oman da kuma IMO kafin su shiga sabuwar hanyar da aka ƙirƙiro.
Sanarwar ta zo ne bayan ziyarar da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya kai Oman tare da tawaga ta diflomasiyya.
Hakan kuma ya biyo bayan wata sanarwa ta haɗin gwiwa da Iran da Oman suka fitar, inda suka jaddada ƙudurinsu na tabbatar da cewa mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a buɗe kuma mai aminci ga zirga‑zirgar kasuwanci ta duniya.
Kasashen biyu sun kuma bayyana cewa za su kafa kwamitin haɗin gwiwa domin duba yadda za a tafiyar da mashigar a nan gaba, da kuma tantance kuɗin ayyukan da ake bayarwa ga jiragen ruwa da suke bi ta mashigar.