Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar ƴan ƙwallo: Ƙungiyoyin turai na rububin Wilshare, ƴan wasan United sun sako Ralf Rangnick a gaba
Dan wasan baya na Chelsea Antonio Rudiger, mai shekara 28, ya ce kungiyar ce za ta yanke shawarar ko zai ci gaba da zama ko zai tafi idan kwantiraginsa ya kare a bazara. Tuni dan wasan na Jamus ya samu tayin komawa Real Madrid da Paris St-Germain. (Athletic)
Newcastle za ta sake komawa kan Sevilla a bazara don neman dan wasan baya na Brazil Diego Carlos, mai shekara 28, wanda ta rasa a kasuwar musayar 'yan wasa na Janairu. (Marca)
Kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain na shirin hada kudi mai tsoka domin siyan dan wasan tsakiyar kasar Faransa Paul Pogba a wannan bazarar. Sai dai dan wasan mai shekaru 28 bai yanke hukuncin zama a Manchester United ba, inda Juventus, Barcelona da Real Madrid suma suka sanya ido a kanshi (Mail)
Manchester United ta saka Christopher Nkunku, mai shekara 24, cikin jerin 'yan wasan da take nema a bazara bayan kocin rikon kwarya Ralf Rangnick ya bukaci kungiyar da ta kara zawarcin dan wasan tsakiyar na RB Leipzig na Faransa. (ESPN)
Wasu 'yan was an Manchester United kamar Cristiano Ronaldo ba su yarda Ralf Rangnick na da kwarewar ci gaba da jagorantar kulob din ba. (AS)
Lallashin Cavani da Rangnick ya yi, ya sa Edinson Cavani, mai shekara 35 soke ra'ayinsa na barin Manchester United a watan Janairu. To amma duk da hakan zai tashi a bazara lokacin da kwantiraginsa zai kare. (Fabrizio Romano)
Arsenal ta yi shuri da damar sayen dan wasan gaban Argentina Mauro Icardi, mai shekara 28 daga Paris St-Germain a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu. (Athletic)
Manchester City na daga cikin manyan kungiyoyin Premier da ke son dauko dan wasan Barcelona da Spain Nico Gonzalez, mai shekara 20, wanda ya haska kansa a Nou Camp a bana. (Marca)
Dan wasan gaba na Chelsea da Albania Armando Broja, mai shekara 20, bai yanke hukuncin barin Stamford Bridge a wannan bazarar ba. A halin da ake ciki dai Arsenal na zawarcinsa saboda rawar da ya taka a Southampton a inda ya je a matsayin aro (Express)
Kungiyar Como ta Seria B da kungiyoyin da ke gasar Super League ta Girka na sha'awar sayen dan wasan tsakiyar Arsenal Jack Wilshere, mai shekara 30, wanda k atisay da tsohon kulob dinsa Arsenal kuma ya buga wa Ingila wasa a shekarar 2016. (Football London).
Dan wasan tsakiyar Ivory Coast, Franck Kessie, mai shekara 25, bai yanke shawarar kulob din da yake son shiga ba idan kwantiraginsa a AC Milan ya kare a bazara. Yanzu dai Barcelona na cikin masu zawarcinsa. (Fabrizio Romano)
Tsohon dan wasan Manchester United Paul Ince ya ce ya kamata kungiyar ta sayi dan wasan tsakiyar Brighton da Mali Yves Bissouma, mai shekara 25, domin maye gurbin dan wasan Brazil Fred, mai shekara 28. (Metro)