Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Haaland, Phillips, Rangnick, De Jong, Costa, Carlos, Lingard
Tilas Real ko Barcelona ta kashe makudan kudi idan suna son raba Erling Braut Haaland daga Borussia Dortmund. Wannan ya hada da kudin sanya hannu na dan wasan mai shekara 21. (Marca)
Liverpool na son rana Kalvin Phillips dan wasan tsakiya mai shekara 26 da kungiyarsa ta Leeds, sai dai kungiyarsa ba ta son sakinsa., inda har Paris St-Germain, Bayern Munich da Real Madrid duka na sha'arwa sayensa. (El Nacional - in Catalan)
Sai Chelsea ta kara yawan kudin da ta yi wa Barcelona kan dan wasan tsakiya Frenkie de Jong. Tun farko ta yi tayin fam miliyan 33. (El Nacional - in Catalan)
Kocin Manchester United na riko boss Ralf Rangnick ya fara gajiya da yadda kungiyar ta ki sakar ma sa dala domin sayo 'yan wasa, kuma dan kasar Jamus din mai shekara 63 ya damu da halin da zai shiga a karshen kakar wasa ta bana, lokacin da zai mika kungiyar ga sabon koci. (Mirror)
Arsenal na tattaunawa da Chelsea kan daukan Diego Costa mai shekara 33, inda ake sa ran zai bar Atletico Miniero a wannan watan. (Goal - in Portuguese)
Newcastle za ta ci gaba da tattunawa da Sevilla a mako mai zuwa kan dauko Diego Carlos dan wasan baya na Brazil mai shekara 28. (90 Min)
West Ham za ta sha wuya kan kokarinta na dauko Jesse Lingard, inda Newcastle da Manchester United ma ke nuna sha'awarsu kan dan wasan mai shekara 29. (Star)
Barcelona na sha'awar raba Roberto Firmino da Liverpool, wadda ta sa fam miliyan 20 kan dan wasan gaban mai shekara 30. (El Nacional - in Catalan)