Real Madrid za ta buga wasan karshe a La Liga ranar Juma'a

Asalin hoton, Real Madrid FC
Mahukuntan da ke gudanar da gasar La Liga, sun sanar da cewar Real Madrid za ta buga wasan mako na 38 ranar Juma'a 20 ga watan Mayu.
Real Betis ce za ta ziyarci Real Madrid, domin buga wasan karshe a bana a La Liga da za su kece raini a Santiago Bernabeu.
Shi ne wasan karshe da Real Madrid za ta kara daga nan a rufe labulan babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Tuni Real Madrid ta lashe kofin bana kuma na 35 jumulla, ba kungiyar da ta kama kafarta a yawan cin kofin La Liga a Sifaniya.
Ranar 28 ga watan Agusta, Real Madrid ta je ta ci Betis 1-0, kuma Daniel Carvajal ne ya samar mata da maki ukun da take bukata a ranar.
Real Betis mai fatan samun gurbin shiga Champions League a badi tana ta hudu a kan teburin La Liga da maki 64 da tazarar maki uku tsakaninta da Sevilla ta hudu.
Real Madrid mai jan ragamar teburin La Liga na kakar nan ta hada maki 85 ta ci karawa 26 da canjaras bakwai da rashin nasara a fafatawa hudu a gumurzu 37 da ta yi a La Liga ta bana.
Ranar 28 Real Madrid za ta kara da Liverpool a wasan karshe a Champions League da za su yi a Faransa - Real tana da kofin 13, ita kuwa Liverpool tana da bakwai jumulla.
Wasannin mako na 37 da za a buga a La Liga.
Ranar Juma'a 20 ga watan Mayu
- Real Madrid da Real Betis
- Rayo Vallecano da Levante
Ranar Asabar 21 ga watan Mayu
- Valencia da Celta Vigo
Ranar Lahadi 22 ga watan Mayu
- Elche da Getafe
- Deportivo Alaves da Cadiz
- Osasunada Real Mallorca
- Granada da Espanyol
- Barcelona da Villarreal
- Real Sociedad da Atletico Madrid
- Sevilla da Athletic Bilbao









