Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Haaland, Martinez, Nkunku, Tchouameni, Ronaldo, Ramsay
Manchester City na dab da bayyana makuɗan kuɗaɗen da ta ware wajen cimma yarjejeniyar sayo ɗan wasan Borussia Dortmund ɗan kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21, a makon gobe. (Sun)
Liverpool ta sha gabanReal Madrid da Chelsea a fafutukar sayen ɗan wasan Monaco dan kasar Faransa da ke buga tsakiya Aurelien Tchouameni, mai shekara 22. (Marca via Metro)
Arsenal na iya fuskantar koma-baya a kokarin ganin ta sayi ɗan wasan Argentine da ke buga gaba Lautaro Martinez, ganin cewa Inter Milan ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan mai shekara 24. (Gazetta Dello Sport)
Arsenal, Chelsea da Manchester United na zawarcin ɗan wasan RB Leipzig da Faransa da ke buga tsakiya Christopher Nkunku, mai shekara 24, a wannan kakar. (Football.London)
Bayern Munich na shirin gabatar da tayin £15m kan ɗan wasan RB Leipzig Konrad Laimer. (Fabrizio Romano on Twitter)
Sai dai Manchester United ita ma tana sha'awar sayen ɗan wasan mai shekara 24 wanda a baya ya taba aiki tare da kocinsu na riƙo Ralf Rangnick. (Mirror)
Tsohon ɗan wasan tsakiya a Manchester United David Beckham na fatan ɗan wasan gaba dan asalin Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, ya ci gaba da zama a Old Trafford a kakar wasa mai zuwa. (Talksport)
Tsohon ɗan wasan Netherlands mai buga tsakiya Fred Rutten ya bayyana yadda ya yi watsi da tayin mataimaki ga sabon kocin Manchester United Erik ten Hag, yanzu haka ya shirya komawa PSV Eindhoven. (Guardian)
Tottenham Hotspur ta shirya fuskantar kalubale daga ɗan wasan ƙungiyar Bundesliga da Serie A Hellas Verona dan asalin Czech mai buga tsakiya Antonin Barak, mai shekara 27. (Inside Futbal)
Liverpool na fatan doke Leeds da cinikin £4m kan ɗan wasan Aberdeen Calvin Ramsay mai shekara 19. (Goal)
Tsohon shugaban Chelsea da Spurs Andre Villas-Boas na iya zama sabon koci a Moroko, hakan na iya bude kofa ga Hakim Ziyech ya dawo bugawa kasarsa kwallo.(Le360 via Sun)