Atletico 1-0 Real Madrid: Atletico Madrid ta ci gaba da zama ta hudu a La Liga

An wallafa

Atletico Madrid ta yi nasarar cin Real Madrid 1-0 a wasan mako na 35 a gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi a Wanda Metropolitan.

Atletico ta ci kwallon ta hannun Yannick Ferreira Carrasco a bugun daga kai sai mai tsaron raga saura minti biyar su je hutun rabin lokaci a karawar ta hamayya.

Da wannan sakamakon Atletico mai La Liga na bara tana mataki na hudu a teburi da maki 64 da tazarar maki shida tsakaninta da Real Betis ta biyar, kuma saura wasa uku-uku suka rage a kammala wasannin bana.

Real Madrid wadda tuni ta lashe La Liga na bana kuma na 35 jumulla ta yi rashin nasara a wasa na hudu a kakar nan kenan a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Wannan shi ne wasa na biyu da suka kece raini a gasar La Liga ta bana, bayan da Real ta ci Atletico 2-0 ranar 12 ga watan Disamba.

Wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Karim Benzema da ya ci a minti na 16 da kuma Marco Asensio da ya zura kwallo a raga a minti na 57.

'Yan wasan da kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya je Atletico da suka buga wasan na hamayya ranar Lahadi.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V. da kuma Camavinga.

Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Jović, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.