Barcelona ta samu gurbin buga Champions League a badi

An wallafa

Barcelona ta samu gurbin shiga gasar Champions League ta badi kai tsaye, bayan da ta doke Real Betis 2-1 a gasar La Liga ranar Asabar.

Ansu Fati ne ya fara ci wa Barcelona kwallo - kuma na farko da ya zura a raga tun bayan da ya fara jinya daga 6 ga watan Nuwamba.

Sai dai kuma Betis ta farke ta hannun tsohon dan kwallon Barcelona, mai tsaron baya, Marc Bartra.

Saura minti hudu a tashi daga wasan Barcelona ta kara na biyu ta hannun Dani Alves.

Tun kan fara wasan Barcelona ta yi wa Betis tarbar girma, wadda ta lashe Copa del Rey na bana, inda suka yi layi biyu suna musu tafi a lokacin da suke shiga tsakiyar fili.

Betis ta yi nasarar daukar Copa del Rey na kakar nan, bayan da ta doke Valencia a karawar karshe.

Real Madrid wadda ta lashe La Liga na bana kuma na 35 jumulla, tana mataki na daya da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona.

Sai dai kungiyar Camp Nou ta bai wa Betis ta biyar a teburi tazarar maki 11, kuma saura wasa uku-uku a karkare kakar bana.

Barcelona tana mataki na tara a lokacin da Xavi ya maye gurbin koci Ronald Koeman a watan Nuwamba.