An ci tarar Manchester United kan jifan Diego Simeone a Champions League

An wallafa

An ci tarar Manchester United fam 8,420, bayan da magoya baya suka jefi kociyan Atletico Madrid, Diego Simeone a Champions League a Old Trafford.

Simeone ya sha jifa da ta kai ya ruga a guje zuwa dakin hutun 'yan wasa a karawar da Atletico ta ci United 1-0 a wasa na biyu a gasar Zakarun Turai ta bana.

An yi waje da United a Champions League na kakar nan, inda Atletico Madrid ta kai zagayen gaba da cin kwallo 2-1, bayan da kungiyar Old Trafford ta tashi 1-1 a wasan farko a Sifaniya.

Haka kuma hukumar kwallon kafar Turai, UEFA ta ci tarar Rangers fam 38,900 da kuma Liverpool 8,420.

An samu magoya bayan Rangers da kunna abubuwan tartsatsin wuta, an kuma samu kungiyar da laifin da aka fara wasa a latti ranar 7 ga watan Afirilu da Braga ta yi nasara 1-0.

Liverpool kuwa an sameta da laifin haddasa fara wasa ba a kan lokacin da aka tsara ba a Champions League da ta yi nasara a gidan Benfica 3-1, an kuma ja kunnen Jurgen Klopp.

Ita kuwa Galatasaray an bukaci ta rufe wani kaso na filin wasanta zuwa kaka biyu - an samu magoya bayan kungiyar da jefa robobin ruwan sha da kofuna cikin filin wasa a karawa da Barcelona da aka yi ta samun tangarta a fafatawar a Instambul a watan jiya.

Alkanin tamaula ya yi ta tsayar da wasan karo da dama, yayin da 'yan wasan Galatasaray ke ta kwantar da hankalin magoya baya.