KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 23 ga watan Yunin 2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • Sadis Buba

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Abun fashewa ya tashi a wani kasuwa a Lagos

    ....

    Asalin hoton, Screengrab/Lagos Police Command

    Abun fashewa ya tashi a wani sashe na kasuwar Mushin da ke Lagos a ranar Litinin, inda mutum guda ya jikkata bayan wata mota ta tarwatse sakamakon fashewar.

    Lamarin ya faru ne da tsakar dare a wani wuri da ke 22, Oke Mushin, inda aka ajiye motar a cikin kasuwar kayan takalma.

    Mazauna yankin sun bayyana cewa ana zargin wani ne ya dasa abun fashewa (IED) a ƙarƙashin motar da ta tarwatse, amma har yanzu ba a gano mamallakin motar ba.

    Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Fatai Tijani, ya ce sun samu rahoton fashewar, kuma nan take suka tura ƙwararrun jami’an kwance abubuwan fashewa (EOD) zuwa wurin.

    Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa an sanya IED ɗin ne a ƙarƙashin motar a ɓangaren fasinja, kuma ya fashe ne a lokacin da aka kunna injin motar.

  2. Qalibaf da Araqchi sun tafi Oman kan batun Mashigar Hormuz

    Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, tare da babban mai shiga tsakani Abbas Araqchi, sun tafi ƙasar Oman domin tattaunawa kan yadda za a tafiyar da Mashigar Hormuz.

    Rahotanni sun ce Qalibaf ya bar Tehran zuwa Muscat jim kadan bayan dawowarsa daga tattaunawar Iran da Amurka da aka yi a Switzerland, inda batun sarrafa mashigar ya zama muhimmin abu.

    Ana sa ran tawagar Iran za ta gana da Sarkin Oman, Haitham bin Tariq, domin tattauna shirye-shiryen Iran kan kula da mashigar da kuma karfafa hadin gwiwar ƙasashen biyu.

    Wannan na zuwa ne bayan kammala zagayen farko na tattaunawar Iran da Amurka, wanda ya sa tawagar Iran komawa gida kafin sake wasu muhimman ganawa.

    A wani ɓangare kuma, fadar shugaban Iran Masoud Pezeshkian ta sanar da cewa zai kai ziyara Pakistan na kwana guda, domin gode wa kokarin sasanci da kasar ta yi tsakanin Iran da Amurka tare da bunƙasa hulɗar tattalin arziki.

  3. Sojojin Najeriya sun ce sun kuɓutar da mutane 47 daga hannun ISWAP a Borno

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas ta ceto mutum 47, yawancinsu mata da ƙananan yara, da mayaƙan ISWAP suka tsare a yankin Kangarwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno.

    A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa an samu nasarar ceto mutanen ne a ranar 20 ga watan Yuni 2026, bayan wani gagarumin samame da sojojinta suka kai wanda ya tilasta ‘yan ta’addar tserewa suka bar waɗanda suka sace.

    Ya ce hare-haren kasa da na sama da dakarun suka kai wa sansanonin ISWAP a yankin Tafkin Chadi ne ya sa ‘yan ta’addar suka rikice suka bar wuraren da suke, lamarin da ya bai wa wadanda aka tsare damar tsira bayan dogon lokaci a hannunsu.

    A yanzu haka, an kai waɗanda aka ceto wuraren tsaro inda ake basu kulawar lafiya da taimakon jin kai, yayin da rundunar ta sake jaddada ƙudurinta na ci gaba da kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

  4. Iran ta nace kan ci gaba da iko da Mashigar Hormuz

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Iran ta sake jaddada ƙudurinta na ci gaba da iko da Mashigar Hormuz bayan kammala zagayen farko na tattaunawa da Amurka a ƙasar Switzerland.

    Da yake magana da talabijin din gwamnatin Iran yayin dawowarsa daga tattaunawar, babban mai shiga tsakani na ƙasar ya bayyana cewa tafiyar da mashigar ba za ta koma yadda take kafin yaƙin ba.

    Ya ce Iran za ta ci gaba da taka rawa wajen sarrafa zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin, tare da tabbatar da cewa an kiyaye buƙatun ƙasar.

    Haka kuma, ya bayyana cewa Iran da Amurka sun amince da kafa wasu hanyoyin haɗin gwiwa na wucin gadi na kwana talatin, ciki har da layin waya kai tsaye da cibiyar sadarwa, domin sauƙaka zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar.

    A nasa ɓangaren, sakataren kudi na Amurka Scott Bessent ya ce Washington za ta dakatar da takunkumin da ta kakabawa man Iran na tsawon kwanaki sittin, domin bai wa tattaunawar damar ci gaba.

  5. Za a samu mummunan yanayin zafi a Turai yau

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran mummunan yanayin zafi zai addabi sassan Yammacin Turai a yau Talata, inda zafin zai kai matakin da aka daɗe ba a gani ba a tarihi.

    Masana hasashen yanayi sun ce zafin zai ƙara tsanani a wannan makon lamarin da ke haddasa fargaba a ƙasashe da dama.

    A Faransa, an gargaɗi sama da rabin ƴan ƙasar kan mummunan yanayin zafi yayin da aƙalla mutane 18 ne suka mutu sakamakon zafin a ranar Litinin.

    A Birtaniya ma ana sa ran za a fuskanci mummunan yanayin zafi a tarihi a wannan watan na Yuni, inda yanayin zafi zai iya haura digiri 35 a ma’aunin Celsius.

    Haka kuma a Spain da Portugal, yanayin zafi ya wuce yadda aka saba gani a daidai irin wannan lokaci na shekara, inda wasu yankuna ke fuskantar ƙarin yanayin zafi mai tsanani.

  6. Dan majalisar Iran ya yi barazanar zaman dirshan kan rufe majalisa

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani dan majalisar dokokin Iran mai wakiltar Tehran, Kamran Ghazanfari, ya sanar da shirin gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar kasar domin nuna adawa da rufe majalisar da aka yi na tsawon watanni.

    A wani sako da ya wallafa a shafin X, Ghazanfari ya ce wasu daga cikin ‘yan majalisa za su je ginin majalisar da karfe 8 na safe a ranar Lahadi.

    Ya ƙara da cewa idan har suka tarar majalisar a rufe, za su zauna a wajen a matsayin zaman dirshan har sai an sake buɗe ta.

    Dan majalisar ya bayyana kiran nasa ne ga al’ummar Iran, yana mai jaddada cewa rufe majalisar na dogon lokaci ba abin da ya dace ba ne.

  7. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.