Za a koma tsarin baya a cinikayyar 'yan kwallon Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin Premier sun kada kuri'ar amincewa za su mai da tsarin cinikayyar 'yan kwallo ta zama daya da sauran ta Turai.
Kaka kwallon kafa biyu da ta wuce Ingila kan rufe kasuwarta daf da za a bude wasu ta kasashen Turai.
Hakan na nufin za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a 2020 ranar 1 ga watan Satumba kenan.
An kada kuri'ar ne a taron masu hannun jari a gasar Premier League da aka gudanar a Landan ranar Lahadi.
Za a fara cinikayya kenan a farkon watan Agusta a Ingila, bayan da ake ta korafi daga kungiyoyin Premier cewar an raba musu hankali a lokacin cinikayyar da wasu na cin kasuwa wasu kuma an kammala.
Ana kuma sa ran wasu kasashen Turai za su yi sauyi da zai amfani kungiyoyin Turai nan gaba.
Tun baya kungiyoyin Ingila sun yi kukan cewar ana zawarcin 'yan wasansu a wasu kasashen, yayin da su kuma babu damar maye gurbinsu idan sun sayar don an rufe kasuwa a lokacin.
Tun a baya can kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya yi ta kiran a tsara jadawalin cinikayyar 'yan kwallon Ingila domin ta zama daya da ta kasashen Turai.









