Magoya bayan Manchester United sun yi zanga-zangar 'lumana' kan masu kungiyar

Ralf Rangnick

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ralf Rangnick ya ce ya fahimci "korafe-korafen" magoya bayan kungiyar
An wallafa

Magoya bayan Manchester United sun gudanar da "karamar" zanga-zangar "lumana" a wajen filin horas da 'yan wasan kungiyar ranar Juma'a.

Magoya bayan kungiyar kusan ashirin da hudu ne suka suka taru a wajen filin Carrington domin nuna rashin jin dadinsu da iyalan Glazer, wato mutanen da suka mallaki United.

Ana sa ran gudanar da wata zanga-zangar a Old Trafford ranar Asabar kafin wasan Firimiya da United za ta fafata da Norwich.

Ralf Rangnick ya ce magoya bayan kungiyar suna "da 'yancin bayyana ra'ayoyinsu", kuma ya fahimci "korafe-korafensu" game da matsayin kungiyar na bakwai a Gasar Firimiya.

United ta ci wasa uku ne kacal cikin wasa 12 da ta yi a dukkan gasanni - inda ta sha kashi a hannun Everton da ci 1-0 ranar Asabar din da ta wuce - kuma an tabbatar za ta yi kasa da maki 74 da ta samu a kakar wasan da ta gabata.

"Mun san cewa kwallon kafa wasa ne mai kayatarwa da kuma sosa rai," a cewar manajan kungiyar Rangnick. "Ina ganin ya kamata dukkanmu mu fahimci cewa magoya bayanmu ba su ji dadi ba game da matakin da muke a teburin gasa da kuma rawar da muka taka a karawarmu da Everton.

"Sai dai na yi amannar cewa magoya bayanmu su ne suka fi kwazo a Ingila kuma idan har suka yi zanga-zangar lumana kuma idan har suka ci gaba da mara mana baya a filin kwallo, ina ganin suna da 'yancin bayyana ra'ayoyinsu. Na fahimci rashin jin dadinsu."

Wakilin BBC Sport Simon Stone ya bayyana cewa magoya bayan United sun hadu da masu so a sanya musu hannu kan rigunan kwallo inda suka yi tarnaki ga ababen hawan da ke neman shiga filin wasan.

Lamarin ya tilasta aka sauya wa 'yan jairdar da ke halartar taron manema labaran da Rangnick yake gabatarwa hanyar shiga filin hoars da 'yan wasan.

Watakila Shaw ba zai sake fafatawa a kakar bana ba

Luke Shaw injured on the ground during Manchester United's draw with Leicester

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Luke Shaw ya fafata a wasanni 27 a dukkan gasar da United ta buga a kakar wasan bana

Watakila dan wasan United da Ingila Luke Shaw ba zai buga wasa a makonnin karshe na kakar wasan bana ba bayan an yi masa tiyata domin cire wani karfe da aka sanya masa bayan ya karye a kafafunsa a 2015.

Shaw bai fafata a karawar da kungiyar ta sha kashi a hannun Everton a makon jiya ba, mako guda bayan an tilasta masabarin fili a yayin hutun rabin lokaci a wasan da United ta yi canjaras da Leicester.

Rangnick ya ce yana sa rai dan wasan mai shekara 26 zai yi jinyar "akalla mako hudu zuwa biyar".