Ɓarayi sun sace sarƙoƙin mahaifiyata da kyautar Kofin Duniya - Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tsakiyar Manchester United Paul Pogba ya bayyana cewa ɓarayin da suka haura gidansa sun sace masa kyautar da aka ba shi ta lashe Kofin Duniya na 2018.
Ɗan wasan na Faransa mai shekara 29 ya yi magana kan "tashin hankalin da iyalinsa suka shiga mafi muni" a maokon da ya gabata lokacin da aka haura gidansa daidai lokacin da Man United ke fafatawa da Atletico Madrid a gasar Zakarun Turai ta Champions League.
'Ya'yansa ƙanana biyu da mai kula da su na cikin gidan a lokacin.
"Babban abu dai babu abin da ya samu 'ya'yana," kamar yadda ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta Le Figaro.
Faransa ta lashe Kofin Duniya a 2018, bayan ta doke Croatia 4-2 a wasan ƙarshe da aka buga a birnin Moscow na Rasha. Pogba ne ya ci ƙwallo ta ukun.
Da yake magana kan abin da aka sace, Pogba ya ce: "Akwai sarƙoƙi na mahaifiyata, da kyautata ta Kofin Duniya.
"Abin da ya fi tsorata ni shi ne 'ya'yana na cikin gidan tare da mai kula da su a lokacin da lamarin ya faru.
"Ta ji komai, sannan ta kira matata da jami'an tsaro, daga baya kuma ta kulle kanta da yaran a cikin ɗaki. Ta shafe kwanaki cikin kaɗuwa.
Pogba ya kasance a Man United tun bayan da ya koma ƙungiyar kan kuɗi mafi tsada a tarihin ƙwallon ƙafa na fan miliyan 89. Sai dai kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar nan.









