Matan Afirka 'yan gudun hijira da wasan kwallon kafa ya sauya rayuwarsu a kungiyar Liverpool

Kungiyar na taimakawa lafiyar kwakwalwa, a cewar kociya Comfort Etim

Asalin hoton, Inès Hachou

Bayanan hoto, Kungiyar na taimakawa lafiyar kwakwalwa, a cewar kociya Comfort Etim
    • Marubuci, Daga Samantha Jagger
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Online
  • An wallafa

Ga wata kociya a Liverpool, buga tamaula ya fi komai a kan batun tunanin karawa tsakanin kungiyoyi.

Comfort Etim ta koyi taka-leda ta nuna bajinta lokacin da take tasowa a Najeriya, hakan kuma ya yi tasiri sosai a rayuwarta.

Bayan ta yi hijira zuwa Birtaniya da neman matsuguni, ta lashi takobin cimma burin hada kan mata 'yan gudun hijira a waje guda mai tsaro.

Tana da shekaru 38 a yanzu, kuma ta kasance kociya da abin koyi ga 'yan wasa 30 a kungiyar Toxtethl.

Kungiyar na bayyana Comfort a matsayin macen da take alfahari da ita saboda haɗa-kan mutanen da suka fito daga kasashe daban-daban da rikici ya raba da gidajensu, matsalolin siyasa da garkame su saboda bambanci ra'ayi.

"Fitowa daga yankuna daban-daban a tamaula ya kasance abin burgewa ga wasan," a cewar Comfort, wadda ke zaune a Dingle.

"Ina son na samar da yanayin da matasa za su iya fitowa su yi tsokaci kan rayuwa da zaɓinsu cikin kwanciyar hankali."

Comfort Etim da Kate

Asalin hoton, Inès Hachou

Bayanan hoto, Comfort (a hannun hagu) na horar da tawagar mata su 30, ciki har da Kate (daga hannun dama)

Bayan gwagwarmayar da ta sha wajen neman mafaka a Birtaniya, Comfort ta ce abokan wasanta na zuwa gare ta kuma tana kokarin hada su da kungiyoyin da suka dace.

"Mun zama 'yan uwan juna. Muna tsayawa juna da taimakekeniya da taya juna murna ko bakin ciki," a cewarta.

"Na kasance abin karfafa gwiwa. Akasarin matan na zuwa waje na domin neman shawarari."

'Mu ma muna iya gwada sa'armu'

Hane Leshaj

Asalin hoton, Inès Hachou

Bayanan hoto, Mai tsaron baya Hane Leshaj ta ce kungiyar na taimaka mata ta fannoni daban-daban

Hane Leshaj, wadda ke tsare raga, ta ce ƙungiyar ta taimake ta sosai "a ɓangarori daban-daban" bayan komawa Birtaniya.

"Da fari abin kamar da wahala, musamman idan ba ka fahimtar harshensu kuma ana baka fam 39 domin rayuwa a kowane mako," a cewar 'yar shekara 33.

"Mata da dama iri na na da burin zama 'yan kwallo, amma da yake sun fito daga yankuna daban-daban, sun gagara cimma burinsu.

"Wannan wani kokari ne na nunawa mutanen da ke da yakinin ba za su iya ba, cewa za mu iya mu ma."

'Kina iya mantawa da damuwarki'

Kate

Asalin hoton, Inès Hachou

Bayanan hoto, Kate ta ce wasan tamaula ya kasance babban 'yanci a garerta

Mai tsaron baya kuma mai tsaron raga kate, 'yar shekara 37, ta yaba wa kungiyar saboda rawar da suka taka a rayuwarta bayan ta haifi jaririyarta.

"Abin da ke zuwa zuciyata lokacin da nake wasa shi ne batun 'yanci," a cewarta.

"Yana taimakawa lafiyar kwakwalwa da jikina da sake dawo mun da farin ciki. Kina iya mantawa da damuwarki a wannan ranar.

"Burina shi ne samar da yanayi mai tsaro da kwanciyar hankali ga mata da yara da ke neman madogara."

'Kwallonkafa na sa mutum farin ciki'

Mansura

Asalin hoton, Inès Hachou

Bayanan hoto, Mansura ta ce tana kaunar tamaula tun tana yarinya

Mansura, yar shekara 30, ta nemi mafaka a Birtaniya a 2018 kuma ta ce tawagar Comfort "ta kawo mata farin ciki da cika mata burinta".

"An yi mun maraba cikin mutuntawa, akwai mogon-bayan abokan arziki da raha," a cewar magoya bayan Liverpool.

"Kwallon kafa na sanya farin ciki da ke zuwa mun tun ina yarinya."

'Karɓar mutane cikin girmamawa'

Kokarin Comfort na samar da wani yanayi mai tsaro ga mata a kungiyarta ya kasance abin da ake magana har a wani shirin kafofin yada labarai.

Wayanda suka kirkiri shiri na musamman kan batun, da suka ambaci sunansu da 'Shado', tawaga ce za ta kunshi masu fafutika da 'yan jarida da masu fitowa a fina-finai.

Sun mayar da hankali wajen haɗa mutane waje guda da bada labaransu ta yada za a bi musu hakokinsu da inganta rayuwa.

"Sannin kowa ne cewa masu neman mafaka na sha wahala sosai da fuskantar wariya, hakazalika a yanayi na rayuwa, kungiyoyi irin wadannan na da muhimmanci sosai wajen shawo kan wadannan matsaloli da bincike tsakanin al'umma," a cewar Isabella Pearce.

"Shi kansa kwallon kafa abu ne da ke kawo hadin-kai, amma wannan kungiyar ta kasance ta daban saboda Comfort.

"Muna fatan cewa abin da ke faruwa a Ukraine zai bude idon mutane kan batutuwa da dama da wahalhalun mutane wajen neman mafaka, sannan karban mutane musamman wadanda suka shiga Birtaniya cikin darajawa abin karfafa gwiwa ne."

Presentational grey line