Champions League: Wainar da ake shirin toyawa a Madrid tsakanin United da Atletico

An wallafa

Kocin Manchester United Ralf Ragnick ya gargadi yan wasansa cewa karawarsu da Atletico Madrid tana da wahala sosai musamman ganin cewa ba a gida suke ba.

Za a buga wasan na yau ne a filin Wada Metropolitano da ke birnin Madrid, kafin a dawo Old Trafford a ranar 15 ga watan Maris.

"Akwai yan wasanmu da ba za su samu tarbar mutunci ba, saboda haka mu shirya buga wasa mai zafi. Dama ba hadi bane mai sauki muka samu." In ji Ragnick.

United ta kare na daya a rukunin F, yayin da Atletico wadda ta ci kofin La liga bara kuma suke na biyar a teburi sun kare na biyu a kasan Liverpool a rukunin B.

Sai dai Man United ta je Madrid ne ba tare da dan wasan gabanta ba Edinson Cavani da ya samu rauni.

"Muna da damar kaiwa zagayen gaba na quarter-finals, amma kuma sai mun nuna da gaske muke yi.''

" Akwai bukatar mu nuna cewa karfin mu ya kai. Ba yau Laraba za a gane wanda zai fito ba sai a wasa na biyu.''

''Muna son nuna wa duniya cewa zamu iya cire Atletico Madrid. Kuma idan muka ci kofin Zakarun Turai kai tsaye mun samu tikitin zuwa gasar ta badi.'' A cewar Ragnick.

Sai dai duk da ana ganin United na kwan-gaba-kwan-baya a bana, itama Atletico wasa uku kawai ta ci daga takwas, kuma ta yi rashin nasara har gida makon da ya wuce a hannun Levante.

Kazalika za ta buga wasan ba tare da kyaftin dinta ba wato Koke da ke fama da rauni. Sai kuma Yannick Carrasco da Felipe da aka dakatar.

'' Za mu hadu da daya daga kungiyoyin da ba bu irinsu a duniya,'' a cewar Simeone ranar Talata. A cikin wasanni 14 rashin nasara daya suka yi kuma sirrin shine sabon kocin da suka samu.''

Ya kara da cewa '' Manchester United ta farfado tun bayan zuwan sabon koci. Suna na hudu a tebur, ga zakakuran yan gaba kuma kocin ya hada kansu.''

To amma Simeone ya ce yana da kwarin gwuiwa cewa yan wasansa za su ci su irin yadda ya yadda da su.

'' Wasa ne mai wahala kamar kowane irin wasa a gasar Zakarun Turai. Amma kuma a gida muke tare da yan kallo cike da fili, don bamu samu irin wannan dama ba a 2021 saboda Covid-19.''

A daya wasan na Laraba Benfica za ta karbi bakuncin Ajax a Lisbon.

Duk da ba shine wasan da ya fi jan hankali ba, masu sharhi na ganin wasa ne da zai kayatar, lura da rawar da kungiyoyin suka taka a rukunansu.