Kasuwar yan ƙwallo: Arteta zai ci gaba da zama daram a Arsenal, Madrid na son Mane, Barca na son Dybala

An wallafa

Har yanzu Real Madrid na da kwarin gwiwar daukar dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 23 a kyauta daga Paris St-Germain kuma tana shirin sanar da yarjejeniyar a karshen kakar wasa ta bana. (Goal)

Idan kulob din na Sipaniya ya kasa sayen Mbappe da Erling Braut Haaland na Borussia Dortmund to za su karkata hankalinsu ga dan wasan gaban Liverpool na Senegal Sadio Mane, mai shekara 29. (Fichajes)

Arsenal na sha'awar sayen dan wasan gaban Portugal Joao Felix mai shekaru 22 daga zakarun Spain Atletico Madrid. (El Chiringuito,)

Fatan da Gunners din ke da shi na sayen dan Sergi Roberto daga Barcelona ya kara kaimi ganin cewa har yanzu dan wasan na Spaniya mai shekara 30 bai rattaba hannu kan sabon kwantaragi da kulob din na Catalonia ba. (Sun)

Dan wasan gaban Manchester United dan kasar Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 35, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana, an ce a shirye yake ya saurari tayin kungiyar Botafogo ta Brazil. (Goal)

Newcastle da Aston Villa ne za su jagoranci zawarcin Joe Gomez idan Liverpool ta yanke shawarar siyar da dan wasan bayan na Ingila mai shekara 24 a bazara. (Sports)

Tottenham ta yi tayi mai tsoka kan dan wasan gaba Paulo Dybala mai shekaru 28 daga Juventus a bazara, amma Barcelona da Inter Milan sun kasance zabin dan wasan na Argentina. (Sports).

Crystal Palace na fuskantar fafutuka don ci gaba da rike tsohon dan wasan Faransa Michael Olise mai shekaru 20, wanda Arsenal da Chelsea da Everton ke nema ruwa a jallo da Bayern Munich da Lille. (Sun)

Ana sa ran Liverpool za ta sake sabunta sha'awar dan wasan gaban Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 24, wanda zakarun na Italiya suka ce darajarsa ta kai Yuro miliyan 90. (Calciomercato i)

Arsenal na shirin bai wa kocinta Mikel Arteta sabon kwantiragi na tsawon shekaru uku a bazara a kan fan miliyan 25. (Sun)