Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta casa Lille 2-0 a London, An rike Juventus a Sfaniya
Chelsea da lakadawa Lille kashi 2-0 a gasar Zakarun Turai zagayen kungiyoyi 16 a filin Stamford Bridge.
London Blues sun ci kwallayen ne ta hannun Kai Havertz da kuma Cristian Pulisic a minti na tawkas da kuma 63.
A yanzu Chelsea za ta kai ziyara Faransa wata mai zuwa da kwallaye biyu a hannu.
Chelsea ta buga wasan ba tare da masu tsaron bayanta Ben Chilwell da Reece James ba da ke fama da rauni, to amma Mason Mount ya murmure duk da bai buga wasan ba.
A daya wasan tsakanin Villarreal da Juventus a Sfaniya kunnen doki aka tashi 1-1.
Bakin ne suka fara ci minti shida da fara wasa ta hannun sabon dan wasan gabansu Dusan Vilahovic da suka siyo daga Fiorentina, kafin Dani Parejo ya farke wa Villarreal a minti na 66.
Sai a cikin watan Maris Juventus za ta karbi bakuncin Villarreal a Turin.
A gobe ne za a kwashi yan kallo tsakanin Atletico Madrid da Manchester United a filin Wada Metropolitano da ke birnin Madrid.
Sai kuma na Ajax da Benfica da za a yi a Focugal a filin Estadio do Sport Lisboa.