Afcon 2021: Abin da ya kamata ku sani kan wasannin quarter Final

Cameroon captain Vincent Aboubakar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An shafe shekaru sama da 20 ba a doke Kamaru a gidanta ba.
An wallafa

Za a shiga zagayen quarter final a gasar cin kofin Afirka da ke gudanarwa a Kamaru.

A ranar Laraba aka kammala wasannin zagaye na biyu, kuma bayan wasanni takwas da aka buga, yanzu an tantance kasashe takwas da za su fafata a kwata fainal.

Caf ta musanya wasu filayen da ya kamata a buga wasannin kwata fainal.

Gambia da Kamaru

A ranar Asabar ne Kamaru da ke karbar bakuncin gasar za ta fafata da Gambia.

Karon farko kenan da Gambia ke buga gasar cin kofin Afirka, kuma karon farko da za ta fafata da Kamaru a gasar.

Sai dai an shafe shekaru sama da 20 ba a doke Kamaru ba a gidanta.

Gambia ita ta cire Guinea, kuma ba a doke ta ba tun soma gasar.

Kasashen biyu za su fafata ne a filin Japoma a Douala, misalin karfe biyar na yamma agogon Kamaru da Najeriya

Burkina Faso da Tunisia

Tunisia da ta fitar da Najeriya za ta fafata ne a da Burkina Faso a ranar Asabar.

Kasashen biyu za su gwabza ne a filin Roumdé Adjia a Garoua da ƙarfe 8 na dare.

Masar da Morocco

Wannan haduwa ce ta kasashen Larabawa da ke arewacin Afirka.

Masar wacce ta fitar da Ivory Coast a bugun fanariti za ta kece raini ne da Morocco wacce ta fitar da Malawi.

Za su gwabza ne a Yaounde filin Ahmadou Ahidjo da ƙarfe huɗu na yamma a ranar Lahadi.

Senegal da Equatorial Guinea

Eguatorial Guinea wacce ta yi waje da Mali za ta hadu ne da Senegal a ranar Lahadi.

Kasashen biyu za su ɓarje gumi ne a filin Ahmadou Ahidjo a Yaounde da ƙarfe 8 na dare bayan kammala wasan Masar da Morocco.

Caf ta dawo da lokacin wasan Masar da Morocco zuwa ƙarfe huɗu na rana ne ko da wasan ya kai bugun fanariti don gudun kada ya shiga lokacin wasan Senegal da Equatorial Guinea.

Yadda za a haɗu a zagayen dab da ƙarshe

Gambia ko Kamaru duk wadda ta yi nasara za ta haɗu ne da Masar ko Morocco a zagayen dab da ƙarshe.

Tunisia ko Burkina Faso duk wadda ta yi nasara za ta haɗu ne da Senegal ko Equatorial Guinea a zagayen dab da ƙarshe.

Caf dai ba ta tantance cewa ko za a ci gaba da wasanni a sabon filin Olembe ba a Yaounde bayan rasa rayuka da aka samu.

A nan ake fatan buga ɗaya wasan zagayen dab da ƙarshe da kuma wasan ƙarshe.