Afcon 2021: Ghana ta kori kocinta Milovan Rajevac

Asalin hoton, Getty Images
Ghana ta sallami Milovan Rajevac, bayan da Black Stars ta kasa haura karawar cikin rukuni a gasar da Kamaru ke karbar bakuncin kamar yadda BBC ta faminta.
Ghana ta yi ban kwana da gasar bana, bayan da koci dan kasar Serbia ya samu maki daya a wasannin da ya buga a cikin rukunin da ya kunshi Morocco da Gabon da kuma Comoros.
A karawar da Comoros ta ci Ghana 3-2, shine kasar ya kamata ta yi nasara don samun shiga gurbin zagaye na biyu, amma sai ta kare da maki daya a rukunin bayan karawa uku.
Hukumar kwallon kafara Ghana ta sake daukar Rajevac aiki a mataki na biyu a Satumbar 2021, wanda ya taka rawar gani, bayan da ya kai Ghana zagaye na biyu a wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya.
Sai dai kuma rashin kokarin da Ghana ba ta yi a Afcon a Kamaru ba, Milovan Rajevac ba zai ci gaba da aikin ba.
Ana sa ran za a maye gurbinsa da kocin rikon kwarya a shirin da Black Stars ke yi na tunkarar wasannin karshe don neman gurbin shiga gasar kofin duniya a Qatar a 2022.







