Afcon 2021: Comoros ta fitar da Ghana daga gasar kofin Afirka ta Kamaru

Comoros celebrate

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Karon farko da Comoros ta ci wasa a Afcon da yin waje da Ghana mai kofi hudu, kuma karon farko da ta fara buga gasar
An wallafa

Tawagar Ghana ta yi ban kwana da gasar cin kofin Afirka ta bana, bayan da Comoros ta doke ta 3-2 a wasa na uku a rukuni na uku ranar Talata.

Comoros wadda karon farko ta fara buga Afcon ta fara cin kwallo ta hannun El Fardou Ben Nabouhane daga nan kuma aka kori kyaftin din Ghana, Andre Ayew wanda aka yi wa jan kati.

Ahmed Mogni ya kara cin na biyu kafin daga baya Ghana ta farke kwallayen biyu, wasa ya koma 2-2.

Daga karshe Mogni ya kara na biyu a wasan kuma na uku a karawar a minti na 85 da hakan ya sa Ghana ta yi waje a karawar rukuni a karon farko tun bayan 2006.

Wannan sakamakon zai shiga tarihi a gasar kofin Afirka da ake yi a Kamaru, bayan da Comoros wadda ke buga wasan a karon farko ta yi waje da Ghana mai kofi hudu a tarihi.

Comoros wadda take ta 132 a jerin kasashen da ke kan gaba a taka leda a duniya in ji Fifa, tana da damar zuwa zagayen gaba, bayan da ta hada maki uku a rukuni na uku, wadda ta sha kashi a wasa biyu a jere a cikin rukuni.

Kungiyoyi 12 ne za su kai zagayen gaba kai tsaye, sannan a hada da hudun da suka sami maki mai tsoka don shiga karawar gaba.