Mikel Arteta: Kocin Arsenal ya kamu da korona ba zai jagoranci wasan shi da Man City ba

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An dage wasan Arsenal da Wolves ranar Talata saboda korona
An wallafa

Kocin Arsenal Mikel Arteta zai ƙauracewa wasa da Manchester City a gasar Premier da za su fafata a ranar 1 ga Janairu bayan gwaji ya tabbatar da ya kamu da korona.

Mataimakansa Albert Stuivenberg da Steve Round za su jagoranci wasan a Emirates.

Calum Chambers da Cedric Soares da Takehiro Tomiyasu da kuma Ainsley Maitland-Niles dukkaninsu ba su buga wasan da Arsenal ta doke Norwich ba a ranar 236 ga Disamba bayan sun kamu da korona.

Arteta ya taba kamuwa da korona a watan Maris na 2020.

Sanarwar da Arsenal ta fitar ta ce "Mikel zai killace kansa bisa sharuɗɗan gwamnati kuma muna masa fatan murmurewa,"

Kocin Aston Villa Steven Gerrard da na Crystal Palace Patrick Vieira dukkaninsu sun ƙauracewa wasannin kirsimeti bayan gwaji ya tabbatar da suna da korona.

Arsenal, da ta lashe wasanninta huɗu da ta buga a baya bayan nan, tana matsayi na huɗu ne a tebur, tazarar maki 12 tsakaninta da City da ke jagorancin teburin Premier.

Pierre-Emerick Aubameyang, ba zai buga wasan ba, saboda ya tafi wakiltar ƙasarsa Gabon zuwa gasar cin kofin Afirka da za a fara farkon Janairu a Kamaru.