Wasu abubuwan da suka faru a Barcelona a 2021

Asalin hoton, Barcelona FC
Ana daf da yin ban kwana da shekarar 2021, wadda itama aka fuskanci kalubale a fanni tamaula a kakar nan.
Kungiyar Barcelona tana fama da na ta kalubalen da take fuskanta a bana da suka hada da cutar korana da matsin tattalin arziki da ssauransu.
Ga gerin abubuwan da suka faru a kungiyar Camp Nou wadda ta buga karawa 57 cikin wata 12 a shekarar 2021 kenan.
Duk da fama da cikas da Barcelona ta fuskanta a 2021, kungiyar ta lashe Copa del Rey.
Ta yi nasara a wasa 31
Barcelona ta buga karawa 57 a 2021 ta ci 31 da canjaras 13 aka doke ta sau 13.
Ta zura kwallo 108 a raga
Barcelona ta zura kwallo 108 a raga, ita kuma aka zura mata 69 a 2021.

Asalin hoton, Getty Images
A karkashin Ronald Koeman da Xavi Hernandez da kuma lokacin kocin rikon kwarya, Sergi Barjuan aka ci Barcelona kwallo 69.
Barcelona ta zura kwallo 12 a ragar Athletic Club
Kungiyar Athletic Bilbao ta karbi kwallo 12 a hannun Barcelona, ciki har da hudu a wasan karshe a Copa del Rey, kungiyar ta Barca ta zazzagawa kwallaye da yawa kenan a 2021.
Haka kuma Bilbao itace wadda ta ci kwallaye da yawa a ragar Barcelona, wadda ta ci bakwai jumulla.
Sauran da Barcelona ta ci kwallaye da yawa a 2021 sun hada da Real Sociedad da kuma Granada da kowacce aka ci 11.
Messi ya ci kwallo 28 a Barcelona a 2021

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi shine kan gaba a cin kwallaye a Barcelona daga 108 da ta zura a raga, wanda yanzu ke taka leda a Paris St Germain.
Wadanda ke biye da shi a cin kwallaye sun hada da Antoine Griezmann mai 15 da Memphis Depay mai takwas da Frenkie de Jong mai bakwai da kuma Ousmane Dembele mai shida a raga.
Busquets ya yi wa Barca wasa 56
Sergio Busquets ne kan gaba a yawan buga wa Barcelona wasanni a 2021 da ya yi 56, kuma wasa daya ne bai buga ba a La Liga da Athletic cikin Janairu.
Wadanda ke biye da shi sun hada da Frenkie de Jong da Marc Ter Stegen da kowanne ya yi karawa 52.
Barcelona ta yi amfani da 'yan wasa 37 a 2021
A shekarar da muke yin ban kwana da ita, Barcelona ta yi amfani da 'yan wasa 37, sai dai kuma akwai wadanda ba sa kungiyar a yanzu haka da suka hada da Messi, Griezmann, Trincao, Ilaix Moriba, Pjanic, Junior Firpo, Emerson Royal da kuma Konrad de la Fuente.
An yi nasara 30 da Sergio a cikin fili

Asalin hoton, AP
Bayan da shine kan gaba a yawan buga wa Barcelona wasanni, haka kuma an yi nasara 30 da Sergio Busquets a cikin wasa.
Sai Frenkie de Jong da aka ci karawa 29 da shi da kuma Jordi Alba, Marc Ter Stegen da kuma Òscar Mingueza da kowanne aka yi nasara da su a karawa 28.
Haka kuma Sergio da kuma Ter Stegen suna cikin fafatawa 13 kowanne da Barcelona ta yi rashin nasara a fili a 2021.
Sau bakwai Barcelona tana 1-1

Asalin hoton, Getty Images
Sakamakon da Barcelona ta tashi mai yawa shine 1-1 har sau bakwai a 2021, sai kuma 1-0 da yawa da ta dunga yin nasara.
Shekara ta 2021 Barcelona ta yi fama da kalubale da yawa har da na matsin tattalin arziki da ta kai ta rabu da Lionel Messi da Antoine Griezemann da fitar da ita da aka yi daga Champions League ta koma Europa League da sauyin koci.
Shin ko Barcelona za ta loma kan ganiya a 2022?











