'Yan wasan Barcelona da suka je Sevilla buga kwantan La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Sevilla za ta karbi bakuncin Barcelona, domin buga kwantan wasan mako na hudu a gasar La Liga ranar Talata.
Sevilla ita ce ta biyun teburi da tazarar maki shida tsakaninta da Real Madrid, ita kuwa Barcelona tana ta takwas a kan teburin babbar gasar Sifaniya da maki 27.
Tuni kociyan Barcelona ya bayyana 'yan wasan da ya je da su Sevilla, domin fafatawa a filin Sanchez Pizjuan.
Cikin 'yan wasan Barcelona an samu canji daga wadanda suka kara da Elche, inda Gerard Pique zai buga wasan Talata, bayan dakatar da shi da aka yi da kuma Ilias Akhomach, wanda ya canji Yusuf Demir, wanda yake fama da ciwon ciki.
'Yan wasan Barcelona:
Ter Stegen, Pique, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, O. Dembele, Neto, Coutinho, Lenglet, L. De Jong, Jordi Alba, F. De Jong da kuma O. Mingueza,
Sauran sun hada da Umtiti, Eric, Iñaki Peña, Nico, Jutglà, Gavi, Balde, Ez Abde, Álvaro Sanz da kuma Akhomach.
Wadanda ke jinya a Barcelona:
Sergino Dest, Ansu Fati, Martin Braithwaite, Pedri da kuma Sergi Roberto.









