Dan wasan Liverpool Harvey Elliott ya fara yin atisaye

Asalin hoton, EPA
Harvey Elliott ya koma yin atisaye a Liverpool ranar Litinin a karon farko tun bayan da likitoci suka yi masa aiki kan raunin da ya ji.
Dan kwallon mai taka leda daga tsakiya ya ji raunin a wasan Premier League da Liverpool ta doke Leeds United 3-0 ranar 12 ga watan Satumba, sakamakon ketar da Pascal Struijk ya yi masa.
Sai fitar da dan wasan mai shekara 18 aka yi a kan gadon daukar marasa lafiya, daga nan aka garzaya da shi asibiti.
Elliott ya fara yin atisaye ranar Litinin a karon farko tun bayan raunin da ya yi, bayan da Liverpool ke shirin fafatawa da Arsenal a gasar Premier League karawar mako na 12 ranar Asabar.
Liverpool tana mataki na hudu a kan teburin Premier League da maki 22, bayan wasa 11 a babar gasar Ingila ta bana da tazarar maki hudu tsakaninta da Chelsea mai jan ragama.





