Iheanacho ya ci Laberiya kwallo biyu

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya ta doke Liberia da ci 2-0 da daya a wasan farko na share fagen shiga gasar cin kofin duniya na 2022 da za a yi a Qatar.
Dan wasan Leicester City Kelechi Iheanacho ne ya jefa duka kwallaye biyun a raga, inda ya ci ta farko a minti na 22 da fara wasan kuma ya jefa ta biyu bayan minti 44 dab da za a juya hutun rabin lokaci.
Wasan wanda aka buka a filin wasa na Teslim Balogun ya yi wa kocin Najeriya Gernot Rohr daidai ganin cewa duka 'yan wasansa suna nan kalau babu mai yin jinya cikinsu.
Lokacin da take yunkurin zuwa gasar sau hudu a jere sau kuma bakwai a tarihi, Najeriya za ta buga wasanta na gaba ba tare da dan wasan da ya jefa mata kwallayen ba wata Kelechi Iheanacho.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu dai ita ce ta daya a kan jadawalin rukuninta na C yayin da Cape Verde ta yi kunnen doki 1-1 da Central African Republic
Najeriya za ta buga wasanta na gaba ba tare da 'yan wasa takwas ba a ranar Talata mai zuwa, bayan wancin kungiyoyin kwallon kafa na Burtaniya ciki har da na Premier sun ki barin 'yan wasansu zuwa gida.







