Kylian Mbappe ba zai yi wa Faransa wasa da Ukraine da Finland ba

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kylian Mbappe ba zai buga wa tawagar Faransa wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da Ukraine da kuma Finland ba.

Dan kwallon Paris St Germain ya yi rauni ranar Laraba a fafatawar da Faransa ta tashi 1-1 da Bosnia.

Hukumar kwallon kafar Faransa ta ce ''Kyalian Mbappe na jin radadi a kafar sa, bayan tashi wasa da Bosnia a wasan da suka kara a Strasbourg ranar Laraba.

Ta kare da cewar dan kwallon ya bar sansanin tawagar, kuma ba za ta gayyaci wani dan wasan da zai maye gurbin sa ba.

Faransa ce kan gaba a rukuni na hudu da maki takwas, bayan buga karawa hudu a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya.

Qatar ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a 2022, duk da kalubalen da ake fuskanta daga cutar korona.