Euro 2020: Czech ta fitar da Netherlands a kai quater finals

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar jamhuriyar Czech ta fitar da ta Netherlands a gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana, ta kuma kai karawar quarter finals.
Czech din ta yi nasarar cin kwallo 2-0 a wasan zagaye na biyu da suka kece raini a Puskas Arena ranar Lahadi.
Tomas Holes ne ya ci kwallon farko da ka a zagaye na biyu, bayan da suka yi hutu, kuma bayan da aka bai wa Matthijs de Ligt jan kati, sakamakon tare kwallo da hannu don kar ta shiga raga.
An tabbatar da laifin dan wasan Netherlands din, bayan da aka je aka kalli abinda ya faru a na'urar da ke taimakawa alkalin wasan tamaula yanke hukunci.
Daga baya ne Holes ya bai wa Patrik Schick kwallo, wanda bai bata lokaci ba wajen zura ta a raga saura minti 10 a tashi daga wasan.
Netherlands din wadda ta ci gaba da buga karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili ta samu damar da Donyell Malen ya yi gaba da gaba da mai tsaron raga Tomas Vaclik, amma ya kasa zura ta a raga.
Da wannan sakamakon Jamhuriyar Czech za ta buga wasan daf da na kusa da na karshe da Denmark ranar Asabar 3 ga watan Yuli.
Jamhuriyar Czech za ta ziyarci Azerbaijan don karawa da Denmark a quarter finals, wadda ta doke 3-0 a Euro 2004.












